N300 yake bani don ciyar da yara 8 - Matar aure ta sanar da kotu

N300 yake bani don ciyar da yara 8 - Matar aure ta sanar da kotu

- Wata matar aure mai suna Zainab Abdullahi ta maka uban yaranta takwas a gaban kotun shari'ar Musulunci da ke Maganin Gari

- Mahaifiyar yaran takwas ta bukaci a tsinke igiyar aurensu da mijinta don shekarun shi uku kenan da ya dauka baya zuwa gidan da suke

- Magidancin mai sana'ar facin ya ce rashin samun kudi wajen sana'arshi ne yasa baya kula da iyalin shi amma kotu ta bashi dama zai sauya hali

Wata matar aure mai suna Zainab Abdullahi ta maka mijinta Usman Abdullahi a gaban kotun shari'ar Musulunci da ke Magajin Gari a Kaduna. Ta zargi mai sana'ar facin da bata N300 don kula da yara takwas da suka haifa.

Matar mai zama a Rigasa da ke Kaduna, ta ce mijin nata ya barsu na shekaru uku kuma baya biyan kudin hayarsu har N35,000.

"Ni da babban danmu mai shekaru 22 ne muke hada kudi don biyan haya. Ina rokon kotun nan mai daraja da ta tsinke igiyar aurensu idan ya ki sauya hali," tace.

Wanda ake karar mai suna Abdullahi, ya sanar da cewa yana iya bakin kokarin shi wajen ganin iyalan shi sun zauna cikin walwala da dan kudin da yake samu daga sana'ar shi.

"Wata rana ina basu N900 amma idan babu aiki sosai ranar na kan basu N700, N400 ko N300. Amma yanzu zan sauya in dinga basu N1,000," yace.

N300 yake bani don ciyar da yara 8 - Matar aure ta sanar da kotu

N300 yake bani don ciyar da yara 8 - Matar aure ta sanar da kotu
Source: UGC

KU KARANTA: Sha'awar juna ce ta kama mu muka yi lalata - Wanda yayi garkuwa da matar aure

Mai shari'a Murtala Nasir, bayan sauraron dukkan bangarorin, ya umarci wanda ake karar da ya dau cikakken nauyin iyalansa.

Ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 23 ga watan Maris kuma ya umarci wanda ake karar da ya koma kwanciya a dakin matar shi har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron karar don ganin ko za a samu wani sauyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel