An samu kwayar cutar Coronavirus a jikin mutane hudu a Legas

An samu kwayar cutar Coronavirus a jikin mutane hudu a Legas

Gidan talabijin na Channels 24 ya rawaito cewa an tabbatar da samun kwayar cutar Cronavirus a jikin mutane hudu a jihar Legas.

Kwamishinan lafiya a jihar, Farfesa Akin Abayomi, ne ya sanar da hakan yayin ganawarsa da manema labarai.

Abayomi ya bayyana cewa an samu mutane hudun ne daga cikin mutane 19 da aka yi wa gwajin kwayar cutar a ranar Laraba.

Ya kara da cewa an kebe mutanen hudu da aka samu da cutar a asibitin cututtuka masu yaduwa da ke Yaba, Legas.

Ya ce daga cikin sabbin mutanen da aka samu dauke da cutar akwa wata mata da ta kamu da kwayar da cutar daga wurin mata da ta zo daga kasar Ingila kwana biyu da suka wuce.

A cewarsa, akwai kuma wata mata da ta dawo Najeriya daga kasar Faransa ranar 14 ga watan Maris a jirgin kasar Turkiyya, TK1830.

Na uku daga cikin sabbin masu dauke da kwayar cutar, wani likita ne dan Najeriya da bai fita zuwa ko ina ba, amma aka same shi dauke da kwayar cutar.

Abayomi ya ce na hudun ma namiji dan Najeriya da aka gwada bayan ya dawo daga birnin Frankfurt, kasar Jamus, ranar 13 ga watan Maris.

An samu kwayar cutar Coronavirus a jikin mutane hudu a Legas
Dakin gwajin kwayar cutar Coronavirus
Asali: Facebook

Kafin samun labarin karin mutanen hudu da suka kamu da cutar, a yau, Alhamis, ne gwamnatin jihar Legas ta sanar da cewa ta bayar da umarnin a rufe dukkan kanana da manyan makarantun jihar domin dakile yaduwar kwayar cutar coronavirus.

Kazalika, a ranar Laraba ne gwamnonin jihohin arewa maso yamma, su 7, suka gudanar da wani taro a Kaduna tare da yanke shawarar cewa za a rufe makarantun yankin na tsawon kwanaki 30 don a shawo kan yaduwar cutar Coronavirus.

DUBA WANNAN: Ka yi aiki da wadannan shawarwari 3 cikin gagga wa - Shehu Sani ya yi kira ga Buhari

Sakamakon bullar mugunyar cutar a fadin duniya, an samu faduwar farashin danyen man fetur wanda hakan ya janyo rage farashin kudin litar mai a Najeriya.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa alamu na nuni da cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da rage farashin litar man fetur zuwa N125 daga tsohon farashinsa, N145.

A cewar 'The Nation', majiyarta a fadar shugaban kasa ta sanar da ita cewa shugaba Buhari zai amince da bukatar rage kudin farashin litar man bayan karamin ministan man fetur na kasa, Timipre Sylva, ya gabatar da bukatar neman yin hakan yayin zaman majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da ake yi duk sati a fadar shugaban kasa.

A cewar majiyar, wacce bata amince a ambaci sunanta ba, Sylva ya gabatar da bukatar rage farashin litar man fetur din ne biyo bayan zabgewar farashin danyen man fetut a kasuwar duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel