Bayan bacewar mijinta da dadewa, ta ganshi tare da karuwarshi dauke da tsohon ciki

Bayan bacewar mijinta da dadewa, ta ganshi tare da karuwarshi dauke da tsohon ciki

- Daga karshe dai wata mata da ta dauka watanni tana neman mijinta ta samu ganinshi

- Amma kuma sai ya bayyana mata a halin da bata taba tunani ba kuma bata yi fata ba

- Ta samu mijin nata ne tare da karuwar shi dauke da tsohon ciki a Ibadan, jihar Oyo

Wani jami'in dan sanda wanda ya bace a watan Nuwamban 2019, ya bayyana. Bincike daga bisani sun bayyana cewa ba bata yayi ba tun farko.

A wata wallafa da wata budurwa tayi a shafinta na Twitter, ta bada labari dalla-dalla na jami'in dan sandan son kuwa makwabcinta ne.

Kamar yadda tace, mutumin ya bace ne kuma hakan ya matukar tada hankalin matar shi. Matar ya rame sosai sakamakon azumi da addu'o'in da ta dinga yi wa mijinta a kan ya dawo gida.

Ta kara da bayanin cewa addu'ar ta karbu ne a ranar 17 ga watan Maris din shekarar nan don ta hadu da mijinta a Ibadan da ke jihar Oyo.

Amma kuma labarin bai zamo mai dadi gareta ba saboda tare da wata mata aka ga mijinta. An gan shi ne da karuwar shi wacce ke dauke da tsohon ciki.

KU KARANTA: Sha'awar juna ce ta kama mu muka yi lalata - Wanda yayi garkuwa da matar aure

A wani labari na daban, wani mai garkuwa da mutane mai shekaru 27 mai suna Saidu Iliya da ke kauyen Gada Yeregi a karamar hukumar Lavun ta jihar Neja, ya bayyana yadda yayi lalata da wata mata mai matsakaicin shekaru.

Iliya yayi garkuwa da matar ne kuma sai yayi lalata da ita yayin da yake jiran mijinta ya biya kudin fansa. Sa'ar shi ta kare ne a yayin da wata rundunar hadin guiwa ta 'yan sanda da 'yan sintirin da ke kauyen Vunu suka kama shi.

A lokacin da aka tambayeshi ko ya yi amfani da kwaroron roba wajen lalatar da yayi da ita, sai yace, "banyi amfani dashi ba don da yardar juna muka yi ba fyade nayi mata ba."

An gano cewa, a ranar 5 ga watan Maris ne wani Mohammed Sani da ke sansanin Fulani na Vunu da ke Luvun ya kai rahoton cewa wasu mutane dauke da makamai sun kai hari gidan shi inda suka sace matar shi.

Jaridar Northern City News ta gano cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci naira miliyan 10 na kudin fansa amma daga baya sai suka sasanta a naira dubu dari shida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel