Suna ta yaudarata a kan zanyi arziki - Matashin da ya bankawa coci 3 wuta

Suna ta yaudarata a kan zanyi arziki - Matashin da ya bankawa coci 3 wuta

- A halin yanzu rundunar 'yan sanda na rike da wani mutum da ake zargi da kona coci uku a cikin birnin Kira a yankin Wakiso

- Kamar yadda jaridar Independent ta ruwaito, gobarar da ya haddasa ta kone littatafai, bibul, labulaye da kujerun roba da zasu kai darajar Shs 1.5 million

- Binciken farko ya bayyana cewa wanda ake zargin ya shiga cocin Noah din ne ta taga. Ya tattara kayan waje daya sannan ya watsa musu fetur inda suka kurmushe

A halin yanzu rundunar 'yan sanda na rike da wani mutum da ake zargi da kona coci uku a cikin birnin Kira a yankin Wakiso.

Reagan John Ngobi, mazaunin Namugogo ne kuma ana zargin shi da bankawa cocinan St. Noah Catholic Church Kasokoso, Liberty Church of Christ International da kuma God's Tour Promising Church duk a Uganda a ranakun karshen makon nan.

Kamar yadda jaridar Independent ta ruwaito, gobarar da ya haddasa ta kone littatafai, bibul, labulaye da kujerun roba da zasu kai darajar Shs 1.5 million.

Binciken farko ya bayyana cewa wanda ake zargin ya shiga cocin Noah din ne ta taga. Ya tattara kayan waje daya sannan ya watsa musu fetur inda suka kurmushe.

Luke Owoyesigyire, mataimakin kakakin rundunar 'yan sandan Kampala, yace wanda ake zargin ya mika kanshi ga 'yan sandan da kanshi.

Suna ta yaudarata a kan zanyi arziki - Matashin da ya bankawa coci 3 wuta
Suna ta yaudarata a kan zanyi arziki - Matashin da ya bankawa coci 3 wuta
Asali: UGC

KU KARANTA: Bana bukatar aure don mahaifina yana lalata dani, bana dana-sani - Budurwa

Kamar yadda Owoyesigyire ya bayyana, wanda ake zargin ya amsa laifin shi na bankawa cocin uku wuta don suna wa'azin arziki da wadata amma har yau fatara da talauci na damunshi.

'Yan sanda sunce wanda ake zargin ya yi amfani da lita biyu na fetur don aikata abinda yayi niyya.

Owoyesigyire ya ce, wanda ake zargin ya sanar da masu binciken cewa ya dau wukake ne don kariya ga kanshi koda wani zai hana shi aikata abinda yayi niyya. Ya ce za a duba lafiyar kwakwalwar wanda ake zargin don tabbatar da cewa ba mahaukaci bane.

'Yan sandan sun sanar da cewa, John Reagan Ngobi mai shekaru 21 ya sanar dasu cewa ya fusata ne saboda har yanzu yana cikin halin talauci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng