Tirkashi: Samari biyu sun bayyana dalilin kashe abokinsu dan luwadi

Tirkashi: Samari biyu sun bayyana dalilin kashe abokinsu dan luwadi

- Wani matashi mai shekaru 28 wanda ya kashe abokin shi na Facebook ya bayyana dalilin shi na yin hakan

- Ya ce abokin ya takura shi ne don su yi luwadi kuma ya amince da alkawarin zai biya shi har N20,000

- Bayan zuwan shi ne ya gane cewa bashi da niyyar bashi kudin wanda hakan ya jawo musu fadan da ya buga mishi sanda har ya mutu a take

Wani matashi mai shekaru 28 wanda ya kashe abokin shi na kafar sada zumuntar Facebook tare da yadda gawar a daji da ke Nanka a jihar Anambra, ya bayyana dalilin shi na yin hakan.

Wanda ake zargin mai suna Angus Chukwuebuka Nwankwo da dan uwanshi mai suna Chidiebere Omeyi an kama su ne da laifin kisan wani mutum dan luwadi.

Nwankwo ya ce ya hadu da mamacin ne a kafar sada zumunta Facebook inda suka amince zasu hadu a Nanka don yin aikin ashsha.

An gano cewa matasan biyu sun je yadda gawar mutumin ne a daji yayin da aka kama su suna aikatawa.

A yayin bayyana dalilin da yasa suka kashe mutumin, Nwankwo yace: “Mun hadu a Facebook ne kuma ya tambayeni ko ina luwadi amma sai ance mishi a’a. Bayan takura ni da yayi sosai sai na amince mishi. Ya yi alkawarin biyana N20,000 bayan mun kammala.

Tirkashi: Samari biyu sun bayyana dalilin kashe abokinsu dan luwadi

Tirkashi: Samari biyu sun bayyana dalilin kashe abokinsu dan luwadi
Source: UGC

KU KARANTA: Zan iya auren duk yawan matan da nake so don ni Musulmi ne - Tsohon dan majalisar tarayya

“Yana isowa kuwa nace ya fara bani kudin amma sai yace sai na fara kwantar mishi da sha’awa sannan zai biya ni don tun daga jihar Imo ya zo neman hakan.

“Daga nan ne fa muka fara dambe kuma shi ya fara dukana da sanda har na fadi kasa. Dan uwana ne ya taimaka min na tashi tare da samun sandar da na buga mishi wanda hakan ne yayi sanadiyyar mutuwarshi a take.”

A yayin zantawa da manema labarai, wadanda ake zargin sun musanta yasar da gawar mutumin a daji. Sun ce da kansu suka mika kansu ga ‘yan sintiri wadanda suka kai su har wajen runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami a nNanka don kuwa basu da ofishin ‘yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel