Abinda yasa aka tsige Sarki Sanusi - Tanko Yakasai

Abinda yasa aka tsige Sarki Sanusi - Tanko Yakasai

Alhaji Tanko Yakasai, dan siyasa a arewa kuma daya daga cikin wadanda suka kirkiro Arewa Consultative Forum, ya bayyana dalilin da ya jawo tsige rawanin tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido a ranar 9 ga watan Maris din 2020.

A wata tattaunawa da aka yi da shi da jaridar Punch a ranar Lahadi, Yakasai ya ce dalilin farko da yasa aka tsige rawanin sarkin shine yadda ya ke wa wanda ya nada shi sarki biyayya, wato tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso. Wanda tuni kuwa suke da tsananin rashin jituwa da Gwamnan yanzu, Abdullahi Umar Ganduje.

Abu na biyu kuwa da ya jawo tuge rawanin tsohon sarkin shine rashin fahimtar tsohuwar al'adar jihar Kano wanda hakan yasa yake aiki ba tare da dubanta ba.

"An haifeni a Kano kuma na san al'adun masarautar. Tun da nake yaro har zuwa yau, da sarki mai ilimi da mara ilimi basu magana da yawa. Suna mutunta kalamansu. An haifa Sanusi a Kano ne amma tashin Legas ne da Kaduna. Mahaifinsa ma'aikacin gwamnati ne wanda ya kai matsayin babban sakatare.

Abinda yasa aka tsige Sarki Sanusi - Tanko Yakasai
Abinda yasa aka tsige Sarki Sanusi - Tanko Yakasai
Asali: Original

DUBA WANNAN: Yadda diyar Sanusi tayi hasashen tube rawanin mahaifinta

"Al'adar ma'aikatan gwamnati ne balle wadanda ke aiiki a ma'aikatar lamurran kasashen waje na rashin zama a waje daya. Sarkin da farko yana rayuwa ne tare da tsohon ministan tsaro, Alhaji Inuwa Wada amma da mahaifinsa ya dawo sai suka canza shi.

"Sarkin asalinsa dan Kano ne amma bai rayu da jama'ar Kano ba har sai da ya hau karagar mulkin masarautar. Wannan ne tushen matsalar." Yakasai ya sanar da Punch.

Alhaji Yakasai ya kara da cewa, babban dan marigayi sarkin Kano, Ado Bayero ne yafi cancanta da karagar mulkin amma kuma gwamnan lokacin sai ya dora Sanusi.

Kamar yadda ya ce, wani abu da ya kara tunzura gwamnan shine yawan maganar sarkin a kan komai kuma duk ra'ayoyinsa sun ci karo da ra'ayin al'adun jihar Kano din.

Wannan kuwa kamar yadda ya sanar, ya biyo baya ne saboda sarkin bai tashi a cikin Kano din ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel