Dan uwa ya kashe dan uwan shi a kan Aku guda biyu
- Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta damke wani mutum mai shekaru 40 a duniya a kan zargin halaka kanin shi
- Olanrewaju Adeyinka ya sokawa kanin shi fasasshen gilashin taga ne bayan hargitsi ya shiga tsakaninsu a kan Aku guda biyu da kanin ya kawo cikin gidansu
- Olanrewaju yayi kira ga 'yan sandan da su rangwanta mishi don ba da niyya yayi ba kuma aikin shaidan ne
Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta damke wani mutum mai shekaru 40 a duniya mai suna Olanrewaju Adeyinka a kan zarginsa da ake da kashe dan uwan shi.
Ya zargi dan uwan nashi mai suna Gabriel da kawo Aku masu rai guda biyu cikin gidansu da ke yankin Ilaro ta jihar. Hakan yasa kuwa ya soke shi da makami wanda yayi ajalin shi.
Kamar yadda manema labarai suka bayyana, an damke Olanrewaju ne a ranar 12 ga watan Maris kuma ya amsa laifinshi amma ya ce kuskure ne kuma aikin shaidan ne.

Asali: UGC
KU KARANTA: Na fada fashi da makami ne saboda tsananin talauci - Dalibi
Kamar yadda ya sanar, ya dawo gida a ranar kuma ya tarar da Aku har guda biyu wanda hakan ya kawo hatsaniya tsakanin shi da kanin shi. Ya umarce shi da ya gaggauta fitar da su daga gidan.
Daga nan ne fa fada ya harke tsakaninsu wanda yasa har ya dauko gilashin tagar gidansu ya sokawa kanin shi din. Yayi ikirarin cewa yana kokarin kaiwa makwabcinsu fasasshen gilashin tagar ne yayin da dan uwan nashi ya tsokane shi. Hakan kuwa yasa yayi amfani da shi ya soke shi.
Ya roki 'yan sandan da su rangwanta mishi don bai taba niyyar kashe kanin ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng