Wani mahaukaci ya yi wa'azi tare da jawo hankulan mutane a kan fastocin karya

Wani mahaukaci ya yi wa'azi tare da jawo hankulan mutane a kan fastocin karya

- Wani mutum mahaukaci wanda ba a san sunan shi ba ya dage wajen wa'azi game da Yesu tare da bayyana bukatar a gujewa fastoci makaryata da wuta

- A yayin da yake jawabi ga jama'a da suka zagaye shi a tsakad rana, ya sanar dasu a kan su guji fastoci masu mu'ujiza

- Mahaukacin ya kara da cewa duk kudin da aka bashi na sadaka yayin da yake wa'azin, a yi amfani dashi don walwalar mabaratan da ke kan titi

Bidiyon wani mahaukaci wanda ba a san sunan shi ba ya jawo maganganu a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook. A bidiyon kuwa, an ga mutane sun zagaye mutumin yayin da yake musu wa'azin yadda za su samu aljanna.

A haukacen da yake kuma babu takalmi a kafar shi, ya sanar da jama'ar cewa wuta ba wajen zuwan kowa bane don bata da dadi. Jama'ar da wa'azinshi ya ratsa shi, sun dinga ajiye kudin sadaka a gaban mahaukacin.

Wani mahaukaci ya yi wa'azi tare da jawo hankulan mutane a kan fastocin karya (Bidiyo)

Wani mahaukaci ya yi wa'azi tare da jawo hankulan mutane a kan fastocin karya (Bidiyo)
Source: Twitter

KU KARANTA: Na fada fashi da makami ne saboda tsananin talauci - Dalibi

Mahaukacin ya kara da kushe fastocin karya masu damfara da mu'ujiza. Ya bukaci mutane da kada su yadda da irinsu tare da kiransu da "wakilan shaida" wadanda ke yaudara ta hanyar kawata wa jama'a mu'ujizojinsu na karya.

Ya sanar da jama'ar cewa baya bukatar kudin sadakar da suke ajiyewa amma ayi wa mabaratan kan titi amfani dashi don walwalarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel