Na fada fashi da makami ne saboda tsananin talauci - Dalibi

Na fada fashi da makami ne saboda tsananin talauci - Dalibi

- Wani dalibi mai suna Promise Agonwu dan asalin jihar Ribas ya bayyana cewa ya fada fashi da makami ne don tsananin talauci

- Promise dai dalibi ne a shekara ta biyu a fannin karantar na'ura mai kwakwalwa amma sai ya fada kungiyar fashi da makami

- A samamen da rundunar 'yan sandan ta kai a kananan hukumomi biyu na jihar, sun samu damko bata-gari 20 tare da tarwatsa sansaninsu a dazuzzukan jihar

Wani mutum wanda ake zargi da fashi da makami mai suna Promise Agonwu dan asalin karamar hukumar Etche ta jihar Ribas, ya amsa laifin shi na zama dan fashi da makami.

A yayin amsa laifin shi, Agonwu wanda dalibi ne a sashen karantar na'ura mai kwakwalwa, yace ya fada harkar fashi da makami ne don fatattakar talauci.

Ya ce: "An kama ni ne saboda na shiga kungiyar 'yan fashi da makami. Mun yi fashin ne a Agip da ke Fatakwal.

"Na fada harkar ne saboda talauci. A halin yanzu ina aji biyu a fannin karantar na'ura mai kwakwalwa."

Kwamishinan 'yan sandan jihar Ribas, Mustapha Dandaura, wanda ya damko wanda ake zargin tare da wasu mutane biyar, ya ce sun kama su ne a dajin Obibi da ke Etche yayin wani samame da suka kai.

Ya ce an samu bindigogi kirar AK 47, fisto da harsasai har carbi shida.

Na fada fashi da makami ne saboda tsananin talauci - Dalibi
Na fada fashi da makami ne saboda tsananin talauci - Dalibi
Asali: UGC

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa tayi martani a kan 'harin' da aka kaiwa Buhari a Kebbi

"Jami'an 'Operation Sting' tare da hadin guiwar wasu cibiyoyin tsaro, sun yi aikin makonni biyu cif na kai samame a kananan hukumomin Khana da Gokana. Sun samu isa sansanin bata-gari biyu kuma sun tarwatsa a kalla sansani 20 na 'yan ta'adda a dajin Ogoni."

"Mun samu bindigogi hudu kirar AK 47, fiston daya, carbin harsasai bakwai, bindigar katako daya, layoyi da kuma bindigun roba biyu.

"A kuma wani shiryayyen samame da jami'an runduna ta musamman suka kai, sun zazzage dazuzzukan Rumuji Emuhua, Ogbakiti, Rumuodogo da Ndele inda bata-gari suka yi katutu.

"Aikin jami'an tsaron ya dauka makonni biyu wanda hakan yasa aka damke masu garkuwa da mutane, 'yan fashi da makami sannan kuma sun samu makamai masu tarin yawa. A wannan lokacin ne suka halaka Ekwueme Brown, wanda aka fi sani da 'Shaidan' a wata musayar wuta da aka yi tsakanin 'yan sandan da bata-garin." ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel