Sirikina ne ya bukaci in samo masa sassan jikin mutum - Wanda ake zargi

Sirikina ne ya bukaci in samo masa sassan jikin mutum - Wanda ake zargi

- A ranar Alhamis ne rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta kama wasu da ake zargi da addabar jihar a cikin kwanakin nan

- Daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Idris Sule, an kama shi ne da sassan jikin dan Adam

- Ya bayyana cewa sirikin shi wani Alhassan ne ya bashi kwangilar samo sassan jikin dan Adam amma ya samu mataccen mutum ne ba shi ya kashe ba

A ranar Alhamis ne rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta kama wasu da ake zargi da addabar jihar a cikin kwanakin nan.

Daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Idris Sule, an kama shi ne da sassan jikin dan Adam. An zarge shi da cire kai tare da hannayen wani mutum wanda ba a sani ba a Isua Akoko da ke karamar hukumar Akoko ta Kudu maso gabas. Ya kuma adana sassan jikin ne a kauyen Shinabole da ke karamar hukumar Ose ta jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Tee-Leo Ikoro, wanda ya damko Sule, ya ce ana kyautata zaton ya aikata laifin ne tun makonni biyu da suka gabata.

Ya ce, "Wani mai suna Ahmed Odere mai gona a sansanin Shinabole ya dawo gida amma sai yaji wani irin wari a gidan wanda yake tare da 'yan haya uku. A yayin da aka rasa wanda zai yi bayanin warin sai ya sanar da mai gidan.

"Bayan mai gidan ya biyo shi kuma ya tambayi mutanen gidan dalilin warin. Daga nan sai ya umarcesu da su fitar da duk kayansu don gano inda warin yake.

Sirikina ne ya bukaci in samo masa sassan jikin mutum - Wanda ake zargi

Sirikina ne ya bukaci in samo masa sassan jikin mutum - Wanda ake zargi
Source: UGC

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa tayi martani a kan 'harin' da aka kaiwa Buhari a Kebbi

"Kowa ya fitar da kayan amma kuma Idris Sule baya nan. Bayan an ganshi ne ya fito da kayan shi tare da fito da babban buhu dauke da babbakakken kai da hannayen mutum. Ya ce yaran wani Alhassan Ishaku ne suka same shi a kan cewa mahaifinsu na bukatar sassan jikin mutum.

"Daga nan ne ya samo wani mutum a Isua ya cire mishi kai da hannaye." ya kara da cewa.

"Sirikina ne ya turo yaranshi biyu a kan yana bukatar sassan jikin mutum. Daga nan sai suka nuna min babbakakkiyar gawa a dajin Isua. Ita na cire wa kai da hannaye biyu. Ba ni na kashe mutumin ba," Sule ya ce.

Ya bayyana cewa 'yan sandan sun kama shi tare da sirikinshi Alhassan amma sai jami'an tsaron suka bada belin sirikin.

Amma kuma kakakin rundunar 'yan sandan sun musanta sakin Alhassan da 'ya'yan shi. Sun ce basu kama su ba amma har yanzu suna nemansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel