Annobar Corona ta harbi mai horas da Arsenal, an killace yan kwallon Arsenal duka
Hukumar kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta sanar da garkame filayen atisayenta guda biyu biyo bayan samun tabbacin kamuwar mai horas da kungiyar, Mikel Arteta da annobar cutar Coronavirus.
Legit.ng ta ruwaito Arsenal ta bayyana haka ne a daren Alhamis, 12 ga watan Maris, inda ta bayyana a daren ta samu sakamakon gwajin da aka yi ma Arteta, wanda ya tabbatar da kamuwarsa da cutar.
KU KARANTA: Dawowar bikin al’adun gargajiya na Argungun tabbaci ne na tsaro ya inganta – Buhari
Hakan yasa kungiyar ta killace dukkanin yan kwallonta, tare da wasu jami’an kungiyar da suka yi mu’amala da Arteta a cikin yan kwanakin nan, haka zalika an dage wasan Arsenal da Brighton da za’a buga a ranar Asabar.
A cewar Arteta: “Wannan abin bakin ciki ne, na yi gwajin ne bayan na tsinci kaina cikin halin rashin lafiya, amma zan koma bakin aiki da zarar na an bani dama.”
Ita ma hukumar shirya gasar Firimiya za ta gudanar da taron gaggawa a ranar Juma’a domin tattauna matakin daya kamata ta dauka game da jadawalin wasanni. Sai dai BBC ta ruwaito kafatanin kungiyoyi 20 na Firimiya sun fi so a dage wasannin gaba daya sai wani lokaci.
Kungiyar Arsenal ta fara shiga matsala ne tun a wasanta da Olympiakos da ta karbi bakuncinta a Emirates, a nan ne yan wasan da sauran jami’an kungiyar suka yi cudanya da shugaban Olympiacos wanda daga bisani aka tabbatar yana dauke da cutar.
Sai dai shugaban Arsenal, Vinai Venkatesham ya bayyana cewa: “Kula da lafiyar mutanenmu da sauran jama’a shi ne kan gaba a wajenmu, kuma nan za mu mayar da hankali. Muna tattaunawa da hukumomin da ya kamata don kare yaduwar matsalar, kuma muna sa ran komawa atisaye da zarar mun samu umarnin hakan.”
Idan za’a tuna kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta sanar da tabbacin kamuwar wani dan kwallonta mai suna Daniele Rugani da mugunyar cutar nan ta shaker iska, watau Coronavirus wanda a yanzu ta addabi kasashen Duniya.
Juventus ta bayyana haka ne a ranar Laraba, 11 ga watan Maris, inda ta ce har zuwa yanzu dai Rugani bai fara nuna wata alamar kamuwa da cutar ba, amma gwajin da aka masa ya tabbatar yana dauke da kwayar cutar a jikinsa.
Wannan yasa kungiyar ta dauki matakin killace shi don gudun yaduwar cutar a tsakanin yan wasanta, yan kallo da kuma sauran ma’aikatanta, kamar yadda mahukunta kungiyar suka tabbatar.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng