Bayan shafe shekaru 17 a matsayin manyan abokai, sun gano cewa yaya da kanwa ne

Bayan shafe shekaru 17 a matsayin manyan abokai, sun gano cewa yaya da kanwa ne

- A lokacin da suke yara, suna da wushirya, kasin wuya dakuma launin fata iri daya

- Daga yanayin wakar da suke so zuwa abinda ke birgesu na kyale-kyale, duk iri daya ne

- A ranar 21 ga watan fabrairu, sakamakon gwaji ya bayya cewa Kenny ne maifin Thomas

A lokacin da suke yara, suna da wushirya, kashin wuya da kuma launin fata iri daya. sau da yawa sukan saka takalmi iri daya kuma girman kafarsu daya.

Daga yanayin wakar da suke so zuwa abinda ke birgesu na kyale-kyale, duk iri daya ne. A wani lokaci kuwa, sun yi soyayya da maza biyu 'yan gida daya. Zumuntar tasu babu kamar irinta, Wimberly ya sanar da CNN.

Har zuwa shekaru 17 bayan nan, kusancinsu na nan. Basu taba daukar wuni daya ba, ba tare da sunyi magana da juna a waya ba.

"A manne da juna muke kamar an sa mana gam," Thomas ya ce. Tuntuni dama suna kiran junansu da 'yan uwa na jini. A watan Fabrairu kuwa, sai suka binciko cewa 'yan uwan juna ne su kuma na jini.

KU KARANTA: Sarkin maroka: Mabaracin da ya mallaki gidaje biyar, motoci 20 da kamfanin ruwan leda

Abinda ya fara kawo kokwanto a zukatansu ya faru ne a watan Janairu yayin da Wimberly ta ciki shekaru 29 a duniya. Ta yi liyafa don murnar samun wanda za ta aura.

Thomas mai shekaru 31 ya wallafa hotunan liyafar a Facebook. Wasu daga cikin hotunan suna hade da na Wimberly, mahaifinta da na Kenneth Wimberly.

Bayan wani ya kalla hotunan ne yayi tsokaci yana cewa, "Thomas, mama ta ga hotunan Kenneth kuma ta ganeshi.

"Kawar mahaifiyar Ashley ta bayyana cewa bata san Kenny ne mahaifina ba," Wimberly ta ce.

Babu dadewa kuwa Kenneth ya gano matar. Daga baya kuwa, sai aka nuna mishi hoton mahaifiyar Thomas, wacce a take ya ganeta. A takaice dai sun taba yin soyayya takaitacciya.

A wannan lokacin ne aka gano cewa Thomas ba ta san waye mahaifinta na asali ba kuma aka gano mahaifin Kenneth ne.

A ranar 21 ga watan Fabrairu, sakamakon gwaji ya bayya cewa Kenny ne maifin Thomas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng