Jami'an FRSC sun fasa tayar motar matar da ta dauko mai nakuda (Bidiyo)

Jami'an FRSC sun fasa tayar motar matar da ta dauko mai nakuda (Bidiyo)

- Wani mutum dan asalin garin Fatakwal ya wallafa wani bidiyon jami’an FRSC suna fasa tayar motar ‘yar uwarshi yayin da take kai mai nakuda asibiti

- FRSC din sun zargi matar da kin saka damarar da ke kan kujerar sannan suka ci ta tarar N20,000

- Rashin kudin biyan ne yasa suka sace tayar motar duk da bayanin da tayi musu na cewa kidima ce ta hana ta saka wa

Wani mutum mai suna Port Harcout Cabman, a shafinsa na twitter ya zargi wasu jami’an kiyaye hadurran kan titi da mugunta. Mutumin ya wallafa bidiyo ne inda ya zargi jami’an da fasa wa wata mata tayar mota wacce yace ‘yar uwar shi ce.

Ta bayyana cewa tana hanzarin kai mace mai nakuda asbiti ne saboda kidimewa ta manta bata saka damarar da ke kujerar tukin ba.

DUBA WANNAN: Sarki Sanusi II: Al'ummar unguwar Ja'en sun nesanta kansu daga takardar korafi, zasu yi karar majalisa

Kamar yadda wanda ya wallafa bidiyon ya sanar, laifin ‘yar uwar shi din shine rashin biyan naira dubu ashirin din da suka bukaceta da ta biya.

Ya yi ikirarin cewa ‘yar uwar shi din ba gudu take da motar ba ko kuma tukin ganganci. Hakazalika sun tuhumi matar mai nakudar da rashin saka damarar amma sai ta sanar dasu cewa ba za ta iya jure damarar ba. Saboda tana cikin tsananin ciwon nakuda ne.

A matsayin ladabtarwa kuwa, sai jami’an suka bukaci kudi har naira dubu ashirin amma da suka kasa bayarwa sai suka fasa musu tayar motarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel