Gumina zan more; in ji uwar da ta auri dan cikinta

Gumina zan more; in ji uwar da ta auri dan cikinta

- Wata mata mai shekaru 47 a duniya 'yar asalin kasar Malawi ta auri dan ta mai shekaru 30

- Memory Njemani ta ce wata mata ba za ta morewa guminta ba ta hanyar aure dan nata da ta kashewa makuden kudi

- A halin yanzu, yankin da matar take na kasar Malawi sun yi caa a kanta tare da cewa sai a koneta saboda mayya ce

Wata mata mai shekaru 47 a duniya ta auri dan ta mai shekaru 30. Matar tayi ikirarin cewa ta kashe kudi mai yawa don ilimantar da shi.

Memory Njemani ta ce wata mata ba za ta morewa guminta ba ta hanyar aure dan nata da ta kashewa makuden kudi don ilimantar da shi.

Ta ce lokacin more guminta tare da danta yayi don ta aikatu wajen mayar dashi yadda yake.

Gumina zan more; in ji uwar da ta auri dan cikinta
Gumina zan more; in ji uwar da ta auri dan cikinta
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sarki Sanusi II: Al'ummar unguwar Ja'en sun nesanta kansu daga takardar korafi, zasu yi karar majalisa

"Na zuba kudi mai tarin yawa wajen ilimantar da shi. A kan mene zan ba wata damar more gumina? Wannan ba zai faru ba. Zan auri dan da na haifa ne saboda ba zan habaka wasu matan da suka dinga zubar da cikin 'ya'yansu suka kasa haihuwa ba balle su san dadin 'ya'ya" ta jajanta.

A halin yanzu, yankin da matar take na kasar Malawi sun yi caa a kanta tare da cewa sai a koneta saboda mayya ce.

Jama'a na cewa, asirce dan nata tayi tare da lamushe kurwarsa wanda hakan yasa ya aureta ba tare da ya musanta ba. Dalilan da ta bada kuwa duk na karya ne.

Tuni dai mahaifiyar ta aure dan ta kuma suka fara angwancewa tare da morar junansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel