Coronavirus: Kasar Italiya ta haramta sumba da runguma

Coronavirus: Kasar Italiya ta haramta sumba da runguma

- A birnin Rome na kasar Italia ne a ranar Laraba aka haramta gaisawa da juna wanda za a hada jiki

- Kasar za ta rufe makarantu da jami’o'i daga ranar Alhamis don kokarin shawo kan barkewar cutar

- Wannan kalubalen kuma na bayyana yuwuwar hankada kasar cikin wani halin karayar tattalin arziki tare da tarwatsa kasafin kudinta

A birnin Rome na kasar Italiya ne a ranar Laraba ne suka haramta gaisawa da juna wanda za a hada jiki. An haramta sumba, musabaha da rungumar juna saboda yaduwar cutar coronavirus a kasar.

Sauran matakan da manyan ministocin kasar suka dauka kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka sanar, sun hada da soke duk wasu wasannin kwallon kafa na kasar.

Kasar za ta rufe makarantu da jami’o'i daga ranar Alhamis don kokarin shawo kan barkewar cutar, kamar yadda majiya daga gwamnatin kasar ta sanar yayin da barkewar cutar ke kara yawaita.

Tuni dama aka rufe makarantun yankin arewacin kasar inda cutar ta fi Kamari.

A nahiyar Turai kuwa, kasar Italia ce kasar da ta fi kaurin sunan yada cutar fiye da yankin tsakiyar kasar China inda aka fara samo cutar a watan Disamban shekarar da ta gabata.

Kasar ta fuskanci mutuwa ta 79 sakamakon barkewar cutar wanda hakan yasa ta zama kasa ta uku a duniya da ta samu kamarin cutar bayan kasar China da Iran.

An samu sama da mutane 2,500 da ke dauke da cutar.

Coronavirus: Kasar Italiya ta haramta sumba da runguma

Coronavirus: Kasar Italiya ta haramta sumba da runguma
Source: Instagram

KU KARANTA: Namiji daya ba zai isheni ba, maza 3 zan aura - Jaruma Ifu Ennada

Da yawan mace-macen kuwa ya faru ne a birnin Milan Lombardy da kuma makwatansu na yankin arewa wajen biranen Bologna da Venice.

Amma yankuna 21 cikin 22 na kasar da aka samu cutar na samu kalubalen tattalin arziki a hankali.

A ranar Laraban da ta gabata ne gwamnatin kasar ta yi taron tsari da matakan shawo kan wannan babban kalubalen.

An shawarci mutane da su dinga zama nesa da juna sannan a kiyaye tara taro don gudun yaduwar cutar.

Gaisuwar da suka saba yi a gargajiyance ta runguma ko sumbata a wuya da kumatu duk an haramta su. Wannan kalubalen kuma na bayyana yuwuwar hankada kasar cikin wani halin karayar tattalin arziki tare da tarwatsa kasafin kudinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel