Rashin jituwa: Miji ya nike matar shi da mota a Saudiyya

Rashin jituwa: Miji ya nike matar shi da mota a Saudiyya

- Fada tsakanin ma’aurata dai ya zama ruwan dare a kowanne yanki na duniyar nan

- Akwai labaran fada tsakanin shugabannin kasashe da matansu, sarakuna da matansu, talakawa da matansu

- Wani magidanci ne yayi amfani da motar shi wajen banke matar shi a kan titi bayan sun samu sabani

Fada tsakanin ma’aurata dai ya zama ruwan dare a kowanne yanki na duniyar nan. Dukkan ma’aurata na da banbanci da kuma kamanceceniya a wasu bangarorin rayuwa. Akwai labaran fada tsakanin shugabannin kasashe da matansu, sarakuna da matansu, talakawa da matansu da sauransu.

Babu inda aka isa a hana ma’aurata fada da juna, amma idan an tashi yi, ana yin ba hankali da kuma wanda ba za a yi dana-sani ba.

Wani lamari ne ya faru a watan da ya gabata wanda ya tada hankulan jama’a masu tarin yawa. Ma’aurata ne suke fada a titi amma sai mijin yayi tsananin fushi. Tuni ya shiga motar shi sannan ya tuka tare da banke matar shi din. A nan kuwa ta fadai warwas ba a cikin hayyacinta ba.

Wannan mummunan lamarin ya faru ne a titin birnin Khamis Mushait. Na’urar nadar al’amuran jama’a ce ta dauka sannan ya zagaye yanar gizo.

Rashin jituwa: Miji ya nike matar shi da mota a Saudiyya
Rashin jituwa: Miji ya nike matar shi da mota a Saudiyya
Asali: Twitter

KU KARANTA: An fi kama turawa da laifin ta'addanci fiye da sauran mutane na duniya - Bincike

A cikin bidiyon, an ga mijin na jiran matarshi a yayin da ya nuna zakuwar son yi mata magana. Amma kuma daga baya kawai sai ya shiga motar shi tare da tuka ta inda ya bige matar shi din.

Daga baya kuma sai ga mijin na kallon matar tashi kwance a kan titi ba tare da ta san halin da take ciki ba. Majiya masu yawa sun tabbatar da cewa matar ta samu munanan raunika kuma an kwantar da ita a asbiti. Amma kuma ‘yan sanda sun damke mijin mara iya tankwasa zuciyar shi.

Muna fatan wannan zai zama izinah ga ma’aurata ta yadda zasu kiyaye cutar da juna bayan anyi fada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel