Na dauka mintuna 45 don tabbatar da mutuwarta - Saurayin da ya soka wa budurwa wuka
- Daniel Chukwudiebele Okocha mai shekaru 24 ya shiga hannun jami'an tsaro bayan ya kashe budurwarshi
- Kamar yadda wata majiya ta sanar, saurayin na da tsananin kishi kuma sai ya zargi budurwar da cin amanar shi
- Kamar yadda ya bayyana, sai da ya dauka mintoci 45 bayan soka mata wukar don ya tabbatar da ta mutu
Wani matashi mai shekaru 24 mai suna Daniel Chukwudiebele Okocha wanda ya sokawa budurwar shi mai suna Nkechi Vivian Agwor wuka har ta mutu, a kan zarginta da cin amanar shi, ya shiga hannun rundunar ‘yan sandan jihar Legas.
Lamarin ya faru a ranar Lahadin da ta gabata ne a yankin Egbede da ke Legas. Rashin jituwar ya fara ne bayan saurayin da ke zama da budurwar shi din ya hana ta zuwa coci a ranar Lahadin.

Asali: Twitter
A lokacin da ta nace sai ta je ne sai suka fara fada wanda hakan yasa Daniel ya dau wuka tare da soka mata a wuya sannan ya gudu. A lokacin da aka kama shi kuwa, ya amsa laifinsa na kasheta.
A halin yanzu, wanda ake zargin na sashin binciken manyan laifuka da ke Panti a Yaba.
Wani jami’in dan sanda daya bukaci a sakaya sunansa ya ce: “Daniel ya amsa laifin shi na kisan kai. Ya sanar da mu cewa ya kasheta ne saboda yana zarginta da cin amanar shi.
KU KARANTA: Soyayya ruwan zuma: Budurwa ta tara N1.8m, ta bawa saurayinta kyauta domin ya sayi mota
“Ya sanar da mu cewa a wannan ranar ya hana Nkechi zuwa coci don yana zargin tana bin wani wanda suke zuwa coci daya da shi. Ya ce a lokacin da Nkechi ta ki biyayya kuma ta ce sai ta tafi cocin, sai suka fara fada.
“Daga sakon da ya tura wayarta ne muka gane cewa da gangan ya kasheta. Ya ce sai da ya dau tsawon mintuna 45 don tabbatar da cewa ta mutu. Ya ce ya bata rayuwa mai inganci amma ta ki biyanshi da allheri. Da hakan ne muka gane cewa da ganganci yayi kisan.”
Abun mamakin shi ne yadda suka fito daga gari daya na Ubulu-Uku da ke karamar hukumar Aniocha ta Kudu ta jihar Delta. Binciken farko ya bayyana cewa suna da da daya amma basu yi aure ba.

Asali: Twitter
Mun gano cewa mahaifiyar wacce ta rasun ce ke kula da dan. Hakazalika saurayin na da matukar iko da kuma bakin kishi don ya taba yunkurin kashe kan shi ta hanyar shan gubar Snipper a kan kishi. Budurwar tashi ce ta gaggauta kaishi asibiti inda aka ceto rayuwar shi.
Mahaifin wacce ta rasun, Innocent Agwor, ya ce shi adalci yake bukata. Duk adalcin da za a yi a kan kisar diyar shi ya amince. Ba ya bukatar diyya ko wani kudi na kisanta don ba zai dawo da ita ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng