Namiji daya ba zai isheni ba, maza 3 zan aura - Jaruma Ifu Ennada

Namiji daya ba zai isheni ba, maza 3 zan aura - Jaruma Ifu Ennada

- Tsohuwar jarumar BBnaija mai suna Ifu Ennada ta bada tsokaci a kan irin rayuwar auren da take son yi a nan gaba

- Matashiyar da tayi kudi da gyaran gashi, ta ce tana da burin auren maza uku ne a rayuwarta

- Budurwar dai ta bayyana hakan ne yayin da ta wallafa irin yadda za ta zabi abokin rayuwa a shafinta na Instagram

A wannan sashin na duniya, ba abun mamaki bane idan aka ga namiji da mata masu yawa kuma yana zama tare da su. Wadannan mazan kan yi alfahari da hakan.

Amma kuma sai ga wata mace a Najeriya mai son zama kallabi tsakanin rawuna. Ta ce ita ma tana da burin tara maza don zaman aure ba na bariki ba.

Budurwar mai suna Ifu Ennada, tsohuwar jarumar BBnaija ce a shekarar 2018. Ifu Ennada cikin kwanakin nan ta sanar da masoyanta da mabiyanta na shafinta na Instagram irin rayuwar auren da take sha’awa.

Shahararriyar wacce ta tara arzikin da gyaran gashi, ta ce tana da burin auren maza uku ne a duniya kuma a tare.

Ifu Ennada ta ce: “Ina tunanin zan aura maza uku ne a yadda nake ji yanzu. Tunani na ne nake bayyana muku.”

Namiji daya ba zai isheni ba, maza 3 zan aura - Jaruma Ifu Ennada

Namiji daya ba zai isheni ba, maza 3 zan aura - Jaruma Ifu Ennada
Source: Twitter

KU KARANTA: Vanessa: Mawakiya 'yar kasar Amurka ta Musulunta ta kuma Musuluntar da iyayenta

A wannan wallafar ne take kara bayyana cewa, halin da ta tsinci kanta a ciki ne yasa ta fara kawo wannan tunanin a ranar. Wannan na nuna cewa idan ta tashi aure da zaben abokan rayuwa, maza uku ne cas za ta zaba sannan ta aura kuma su zauna lafiya.

Ifu dai ba yanzu kadai ba take bayyana cewa, ita ba irin wacce ake wa ba’a bace a shafukan sada zumuntar zamani.

A cikin kwanakin nan ne dai Legit.ng ta ruwaito yadda ta caccaki wani mutum wanda ke bibiyar lamurran rayuwarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel