An kashe 'yan sanda biyar, an lalata dukiya a harin Boko Haram a Dapchi (Hotuna)

An kashe 'yan sanda biyar, an lalata dukiya a harin Boko Haram a Dapchi (Hotuna)

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari Dapchi a ranar Laraba inda suka halaka ‘yan sanda 7 tare da wani mutum da ba a gano ko waye ba.

‘Yan bindigar sun kai harin ne wajen karfe 6 na yamma a motoci hudu kirar Toyota Hilux.

Wasu mayakan Boko Haram sun kashe ‘yan sanda biyar a harin da suka kai garin Dapchi da ke arewa maso gabas din Najeriya inda suka sace ‘yan mata 100 a shekarun da suka gabata.

An kashe 'yan sanda biyar, an lalata dukiya a harin Boko Haram a Dapchi (Hotuna)

An kashe 'yan sanda biyar, an lalata dukiya a harin Boko Haram a Dapchi (Hotuna)
Source: Twitter

Mayakan ISWAP din sun isa cikin motoci hudu ne da bindigogi zuwa garin da ke jihar Yobe a ranar Laraba. Tuni kuwa aka fara musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro kamar yadda mazauna yankin suka sanar.

“Da safiyar yau Alhamis ne muka samu gawawwakin ‘yan sanda biyar wadanda suka yi fada da mayakan,” wani mazaunin yankin ya sanar da AFP bayan ya bukaci a boye sunansa.

An kashe 'yan sanda biyar, an lalata dukiya a harin Boko Haram a Dapchi (Hotuna)

An kashe 'yan sanda biyar, an lalata dukiya a harin Boko Haram a Dapchi (Hotuna)
Source: Twitter

“Maharan sun iso ne wajen karfe 5 na yamma kuma sun fara harbe-harbe ne wanda hakan ya ruda kowa,” yace.

Wani mazaunin yankin ya ce ‘yan sandan sun yi artabu da mayakan inda suka kashe biyu daga ciki amma sai mayakan suka fi karfinsu inda suka kashe biyar daga ciki.

An kashe 'yan sanda biyar, an lalata dukiya a harin Boko Haram a Dapchi (Hotuna)

An kashe 'yan sanda biyar, an lalata dukiya a harin Boko Haram a Dapchi (Hotuna)
Source: Twitter

”Muna shirya tawaga don aki gawawwakin Damaturu, babban birnin jihar nan don birne su,” yace.

Mayakan sun yi awon gaba da ababen hawa biyu, daya ta ‘yan sandan dayar kuma ta maharba tare da jami’an tsaro, wani mazaunin yankin ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel