Da mijina na da rai da tuni Najeriya ta wuce yadda ake tunaninta a duniya - Cewar Turai 'Yar Adua

Da mijina na da rai da tuni Najeriya ta wuce yadda ake tunaninta a duniya - Cewar Turai 'Yar Adua

- Turai Musa Yar’adua, matar tsohon shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar’adu ta jajanta halin da kasar nan ke ciki

- Ta jaddada cewa Najeriya da a yanzu ta kai fiye da inda take da mijinta ya kammala wa’adin mulkin shi

- Tsohuwar matar marigayi shugaban kasar, wacce ta sanar da hakan a wani taro na tunawa da tsohon shugaban kasar a jihar Katsina

Turai Musa Yar’adua, matar tsohon shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar’adu ta jajanta halin da kasar nan ke ciki a yau saboda yankewar mulkin mijinta sakamakon rashin lafiya da kuma mutuwar da yayi daga bisani.

Ta jaddada cewa Najeriya da a yanzu ta kai fiye da inda take da mijinta ya kammala wa’adin mulkin shi. Amma kuma sai ciwon ajali ya katse wannan dimbin tanadin da yayi wa kasar nan.

Kamar yadda jaridar Desert herald ta wallafa, “Halin da Najeriya take ciki duk da a yanzu bai kai haka ba. Da ace mijina ya tashi daga ciwon da ya kayar da shi, da an ga aiyukan bada mamaki.

“Duk da cewa mijina ya dade yana ciwo, ya yi iyakar kokarin shi wajen ganin ci gaban Najeriya. Hakazalika an ga rawar da ya taka yayin da yake gwamnan jihar Katsina. Yana da gaskiya da rikon amana kuma ya yarda da jajircewa.” Ta ce.

A yayin bada labarin kankan da kai irin na Musa Yar’adua, ta ce ya taba sanar da ‘yan uwanshi cewa su shirya fada da ita bayan mutuwar shi don tana tunanin ya tara mata dukiya.

Tsohuwar matar marigayi shugaban kasar, wacce ta sanar da hakan a wani taro na tunawa da tsohon shugaban kasar a jihar Katsina, ta kara da cewa: “Marigayi Yar’adua ba shugaba bane mai son abin duniya. A takaice dai baya ta kan wani abu banda bautawa jama’ar kasar nan.

Da mijina na da rai da tuni Najeriya ta wuce yadda ake tunaninta a duniya - Cewar Turai 'Yar Adua

Da mijina na da rai da tuni Najeriya ta wuce yadda ake tunaninta a duniya - Cewar Turai 'Yar Adua
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Fasto ya bawa mabiyansa maganin bera don ya tabbatar da imaninsu sun sha sun mutu

“Akwai lokacin da yace min, Turai ina tausayinki domin idan na rasu za ki samu matsala da ‘yan uwana sakamakon zarginki da za su dinga na killace dukiyar da na bari.”

A yayin bayyana nagartar shi a matsayin shugaba, Turai ta ce marigayin ba ya bada kwangila ba tare da ya adana dukkan kudin da zai biya ‘yan kwangilar ba.

“Akwai lokacin da na tunkare shi a kan maganar da mutane suke yi na cewa a hankali gwamnatin shi ke tafiya. Amma sai yace, mutane za su iya cewa duk abinda suke so amma ba zan bada kwangila ba yayin da banda kudin biya.

"Marigayi Umaru shugaba ne mai matukar adalci don da kan shi yake fita duba aiyuka idan ya bada. Ina tuna lokuta da nake taya shi duba aikin asibitoci da kuma tituna,” ta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel