Masifaffiyar bazawara ta kwakule idon dattijo mai shekaru 73, ya sheka lahira

Masifaffiyar bazawara ta kwakule idon dattijo mai shekaru 73, ya sheka lahira

Wani tsoho mai shekaru 73 mai suna Chief oforbuike Ani dan asalin yankin Amodu Akunanaw a karamar hukumar Nkanu ta yamma a jihar Enugu, ya sheka lahira bayan wata bazawara ta kwakule masa idanunsa biyu.

Bazawarar mai shekaru 38 tana da yara biyar kuma sunanta Blessing Nwatu. An zargeta da make tsohon da bulo a inda yake zaune a farfajiyar gidansa ranar 21 ga watan fabrairun 2020.

Bayan faduwarsa ne Nwatu ta yi amfani da wuka mai kaifin gaske wajen kwakulo idonuwansa kuma ta bar shi kwance a cikin jini.

An gano cewa makwabtansa da suka ga faruwar lamarin ne suka kira daya daga cikin ‘ya’yan Ani wanda ya garzaya da mahaifin nasa asibiti. Ya mutu a ranar 28 ga watan Fabrairun 2020.

Wakilin jaridar The Punch wanda ya ziyarci yankin Okpebe da ke Amodu din a ranar Talata yayin birne tsohon, ya ruwaito cewa mazauna yankin sun kwatanta lamarin da babbar masifa.

Masifaffiyar bazawara ta kwakule idon dattijo mai shekaru 73, ya sheka lahira
Masifaffiyar bazawara ta kwakule idon dattijo mai shekaru 73, ya sheka lahira
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Na kama mijina dumu-dumu yana lalata da matar aure - Matar Liman ta sanar da kotu

Daya daga cikin ‘ya’yan mai rasuwar mai suna Barry, ya ce an kashe mahaifinsa amma kuma wacce ta aikata hakan na hannun jami’an tsaro.

Ya ce, “A ranar 21 ga watan Fabrairun 2020, na samu wayar babban abokin mahaifina a kan in gaggauta zuwa gida don mahaifina bashi da lafiya. A hanyar tahowata ne na fara samun kiran cewa wata mata ce ta kwakule wa mahaifina idanu.

“Bayan isata ne na tarar da mahaifina kwance cikin jini kuma an cire masa idanunsa. Tuni muka garzaya asibiti da shi inda aka dinga kokarin tseratar da rayuwarsa.” Yace.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe wanda ya tabbatar da aukuwar kamarin ya ce, tuni suka damke matar kuma za ta gurfana a gaban kotu a ranar Juma’a mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel