An kone wata mata mai sayar da abinci kurmus bayan an kamata tana amfani da ruwan wankan gawa tana dafa abinci

An kone wata mata mai sayar da abinci kurmus bayan an kamata tana amfani da ruwan wankan gawa tana dafa abinci

- Wata mata mai sayar da abinci ta hadu da fushin matasa inda suka yi mata dukan tsiya kuma suka sanya mata wuta

- Matar dai an bayyana cewa tana amfani da ruwan wankin gawa ne wajen dafawa mutane abinci

- Hakan ya sanya matasan fushi suka kone ta bayan wani mutumi ya tona mata asiri wanda yake aiki a inda take diban ruwan wankin gawar

Wani rahoto da yake ta faman yawo a kafafen sadarwa ya nuna yadda wata mai sayar da abinci daga garin Ughelli, na jihar Delta, ta hadu da fushin matasa, inda suka kone ta kurmus, bayan sun zarge ta da amfani da ruwan wankin gawa tana dafa abincin sayarwa.

Matar mai suna 'Mama Aroma' tayi suna matka a yankin wajen hada abinci mai dadin gaske da mutane ke rububin saya ta ko ina.

Kafin rasuwar ta, matar mai sayar da abinci tana sayar da abinci a cikin mota, inda mutane suke hada dogon layi domin sayen abincin ta mai dan karen dadi.

KU KARANTA: Tsananin talauci yasa matarshi ta gujeshi ta barshi da 'ya'ya 7, sai ga Baturiya ta zo ta aure abin ta

A yadda rahoton ya bayyana, wani ma'aikacin dakin ajiye gawar ya bayyana cewa ya sha ganinta tana zuwa wajen da dare tana diban ruwan da aka wanke gawarwakin dashi, hakan ya sa ya dinga bibiyarta domin yaga abinda take yi da ruwan.

Mama Aroma dai ta shiga cikin tashin hankali, bayan wannan mutumin ya dinga bibiyarta yana ganin abinda take yi da ruwan a kasuwar sai ya sanar da jama'a halin da ake ciki.

Daga baya an ruwaito cewa wasu daga cikin mutanen da suka ci abincin ta sun yi mata dukan tsiya kafin daga baya kuma suka sanya mata wuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel