Auren mace fiye da daya ya fi bibiyar matan banza - Binta ta shawarci maza

Auren mace fiye da daya ya fi bibiyar matan banza - Binta ta shawarci maza

- Zancen auren mace fiye da daya har yanzu yana jawo cece-kuce daga bangarori da dama na Najeriya

- Amma kuma abu daya ne wanda kowa ya san shi, shine mata sun fi maza yawa

- Binta tayi kira ga maza a kan su ji tsoron Allah kuma su auri mace fiye da daya

Zancen auren mace fiye da daya har yanzu yana jawo cece-kuce daga bangarori da dama na Najeriya.

Daga tsokacin da ake samu kuwa, mata na ci gaba da sukar auren mace fiye da daya. Wasu mata ko maza da suke sukar auren mace fiye da dayan na kafa hujjoji ne daga mahangar addinin Kirista.

Amma kuma abu daya ne wanda kowa ya san shi, shine mata sun fi maza yawa. Idan kuwa aka dubi hakan, wa zai auri matan da basu riga sun yi aure ba?

Wani abu da ake mantawa kuwa shine, ba kowanne namiji bane yake iya zama da mace daya ba. Hakazalika, namiji mai shekaru 100 zai iya yi wa mace ciki amma matan masu shekaru da yawa basu iya dauka.

Auren mace fiye da daya ya fi bibiyar matan banza - Binta ta shawarci maza

Auren mace fiye da daya ya fi bibiyar matan banza - Binta ta shawarci maza
Source: Getty Images

KU KARANTA: Kotu ta saki wani dan fashi mata-maza don rashin ma'adanarsa a gidan yari

Wannan lamarin kuwa yasa maza suke fadawa neman matan banza koda kuwa suna da aure.

A yayin da yawaitar zawarawa da kuma neman mata yake ci gaba, wata mata ta shawarci mata a kan mazansu masu yunkurin auren mata su kawo gidansu.

Ta bukaci matan da su saka ransu a cikin salama tare da yarjewa mazansu auren wasu matan.

Ta ce: "Yan uwana maza, ku auri mata a maimakon ku dinga neman mata bayan kuna da aure."

Tayi kira ga maza a kan su ji tsoron Allah kuma su auri mace fiye da daya. Ta kammala da cewa "ku ji tsoron Ubangiji ku auri mata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel