Kotu ta saki wani dan fashi mata-maza don rashin ma'adanarsa a gidan yari

Kotu ta saki wani dan fashi mata-maza don rashin ma'adanarsa a gidan yari

- Wani dan fashi mata-maza wanda aka yankewa hukuncin watanni shida a gidan yari an kasa saka shi wajen mata ko maza

- Rahotanni sun ce Leila Le Fey an yanke mishi hukunci ne saboda barazanar da yayi wa wani mai tsaron shago da guduma don ya samu ya saci giya

- Upton ta sanar da kotun Lewes Crown a kan dokokin gidan yarin na cewa ba a ajiye wani jinsi cakude da wani

Wani dan fashi mata-maza wanda aka yankewa hukuncin watanni shida a gidan yari an kasa saka shi wajen mata ko maza bayan lauyan shi ya musanta ba zai iya zama cikin mata ko maza ba.

Rahotanni sun ce Leila Le Fey an yanke mishi hukunci ne saboda barazanar da yayi wa wani mai tsaron shago da guduma don ya samu ya saci giya.

An kama shi sannan aka garkame na sa'a daya bayan barista Rebecca Upton ta musanta cewa ba shi da jinsin shiga sashin mata ko maza.

Upton ta sanar da kotun Lewes Crown a kan dokokin gidan yarin na cewa ba a ajiye wani jinsi cakude da wani.

Ta kara da cewa: "hanya daya da za a iya gano jinsin shi shine yin gwaji a asibiti," daya daga cikin ma'aikatan kotun ya sanar.

Mutumin mai shekaru 40 ya yi barazana ga manaja Enoch Adetayo da guduma lokacin da ya nemi hana shi satar giya a ranar 6 ga watan Nuwamba, kamar yadda kotun ta ji.

Kotu ta saki wani dan fashi mata-maza don rashin ma'adanarsa a gidan yari
Kotu ta saki wani dan fashi mata-maza don rashin ma'adanarsa a gidan yari
Asali: UGC

KU KARANTA: A karon farko wani Farfesan Najeriya ya bayyana cewa ya samo maganin Coronavirus dana zazzabin Lassa

Kamar yadda Upton ta sanar, Le Fey wanda ke rayuwa a Brighton na fama da sabon shan giya da kwayoyi tun 2014.

Bayan musantawar da Upton ta yi, Mai shari'a Stephen Mooney ya sauya shari'ar inda ya canza hukuncin.

"Ganin illar da hukuncin zai yi, za a iya fuskantar matsaloli a gidan yarin. Na duba cewa ko za a iya jinkirta hukuncin.

"A saboda wannan bayanan, na yanke hukuncin cewa za a mika shi gidan gyaran hali," mai shari'ar ya ce.

Duk da an gano cewa an kama Le Fey da makami kuma yana kokarin fashi wanda kuma ba za a bar shi ya tafi haka ba. An dakatar da zaman gidan yarin na watanni shida har sai ya je gidan gyaran hali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel