Birnin Delhi ya zama mayankar al'ummar Musulmi a kasar Indiya

Birnin Delhi ya zama mayankar al'ummar Musulmi a kasar Indiya

- Kashe-kashen musulmai a kasar Indiya sakamakon hargitsi tsakanin Musulmai da mabiya addinin Hindu ya yi yawa

- 'Yan sanda da sauran jami'an tsaron farin kaya na ta sintiri a titunan a ranar Laraba

- A wannan yankin ne kuma aka samu wata budurwa da ta tsare Doval inda ta sanar da shi cewa ita daliba ce kuma rikicin ya hana ta karatu

Kashe-kashen musulmai a kasar Indiya sakamakon hargitsi tsakanin Musulmai da mabiya addinin Hindu a kan wata doka ya zamo sanadin rasa rayuka 27 a birnin New Delhi a ranar Laraba.

A yayin da babban birnin kasar Indiyan ke fuskantar hari mafi muni a kan Musulmai a wannan lokacin, Firam minista Narendra Modi ya wallafa "Ina kira ga 'yan uwana maza da mata da ke Delhi a kan su zauna lafiya cikin kaunar juna a kowanne lokaci" a shafin shi na tuwaita.

'Yan sanda da sauran jami'an tsaron farin kaya na ta sintiri a titunan a ranar Laraba. Wasu yankunan da aka yi zanga-zanga a su duk an tarwatse.

Modi yayi kiran ne bayan caccakar shi da 'yan jam'iyyun adawa suka yi a kan gazawar gwamnatin shi a wajen dakatar da wannan rikici duk da amfani da barkonon tsohuwa, duwatsu da kuma hayaki da masu zanga-zangar ke yi.

Shugaban jam'iyyar adawa, Sonia Gandhi yayi kira ga ministan lamurran cikin gida, Amit Shah a kan yayi murabus, wanda alhakin aiwatar da doka a babban birnin ya rataya a kan shi.

A wani bangare kuwa, Ajit Doval, mai bada shawara a kan tsaron kasar, wanda alhakin kwantar da tarzomar birnin Delhi din ta rataya a kan shi, ya kara ziyartar Jafrabad a yammacin Laraba don duba yanayin tsaron da kuma yin jawabi ga jama'ar.

"Da izinin Allah zaman lafiya zai wanzu," ya ce a yayin da yake kewaye da tawagar jami'an tsaro.

"An shawo kan komai kuma jama'a sun gamsu. Ina da tabbacin cewa hukumomin tsaro na yin abinda ya dace." Ya kara da cewa.

Birnin Delhi ya zama mayankar al'ummar Musulmi a kasar Indiya

Birnin Delhi ya zama mayankar al'ummar Musulmi a kasar Indiya
Source: Twitter

KU KARANTA: Kotu ta saki wani dan fashi mata-maza don rashin ma'adanarsa a gidan yari

Jafrabad na daya daga cikin yankin da tarzomar ta fi tashi a birnin New Delhi. Kwanaki hudu kenan da ake ta tashin hankulan inda aka kashe mutane 27 tare da raunata mutane 200.

A wannan yankin ne kuma aka samu wata budurwa da ta tsare Doval inda ta sanar da shi cewa ita daliba ce kuma basu iya bacci da dare. Rikicin bai ritsa da ita ba amma kuma bata iya karatu.

"Kada ki damu. Wannan alhakin gwamnati ne da jami'an tsaro. Nayi alkawari," NSA ya sanar da ita.

Doval ya ziyarci babban birnin kasar India din wajen da matsalar ta auku sannan ya gana da jami'an tsaro har da babban ministan Arvind Kejriwal amma tarzomar bata lafa ba. Ya kara da ziyartar Seelampur, Maujpur da kuma Gokulpuri Chowk.

"Mutane na tantamar jami'an 'yan sandan Delhi din amma akwai bukatar a amince da masu khaki," ya ce a lokacin da tarzomar ta sake ballewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel