Kamfanin man fetur na Dangote zai dauki sama da mutane 70,000 aiki

Kamfanin man fetur na Dangote zai dauki sama da mutane 70,000 aiki

- Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya bayyana cewa rashin aikin yi a kasar nan zai ragu

- Gwamnan babban bankin ya sanar da manema labarai ne bayan zagayawa da suka yi a sabuwar matatar man fetur din Dangote a ranar karshen makon

- Dangote ya ce babban kamfanin samar da taki da ke Ibeju Lekki a jihar Legas zai fara aiki a watan Mayu

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya bayyana cewa rashin aikin yi a kasar nan zai ragu. Ya ce matatar man fetur din Dangote za ta samarwa da 'yan Najeriya 70,000 aikin yi idan aka bude shi.

Ya ce sabbin dokokin gwamnatin tarayya za su rage rashin aikin yi a kasar nan.

Gwamnan babban bankin ya sanar da manema labarai ne bayan zagayawa a ranar karshen makon. Ya ce matatar man fetur din Dangoten za ta kara diban wasu ma'aikatan su kai 70,000 bayan 34,000 din da ta diba kafin fara aiki.

Aliko Dangote, shugaban kamfanin Dangote, ya ce ya mayar da hankali ne wajen rage yawan rashin aikin yi da ya addabi kasar nan a gaban shi.

Baya ga samar da aikin yi, hakan zai tabbatar da wanzuwar musaya tsakanin Najeriya da kasashen waje bayan ta samu isassun kayayyakin man fetur.

"Bayan haka, za mu taimaka wajen samar da aikin yi tare da tabbatar da cinikayya kayayyakin kasar nan da kasashen ketare." Dangote ya kara da cewa.

Dangote ya ce babban kamfanin samar da taki da ke Ibeju Lekki a jihar Legas zai fara aiki a watan Mayu.

Ya ce kamfanin takin zai sa Najeriya ta zama ta farko a Afirka kuma babbar kasar da ke samar da taki na dala biliyan 2.5 a duk shekara.

Ya ce: "Nan ba da dadewa bane Najeriya za ta zama kasa ta farko da ke fitar da taki a Afirka a karon farko. Ba fitarwa kadai ba, mai yawa zamu dinga fitarwa."

Kamfanin man fetur na Dangote zai dauki sama da mutane 70,000 aiki

Kamfanin man fetur na Dangote zai dauki sama da mutane 70,000 aiki
Source: Getty Images

DUBA WANNAN: Tirkashi: Na kama mata ta na zina da wani kato a dakin otel - Ahmed Salisu

Dangote yace an fara gwada kamfanin takin kuma zai zama babban kamfanin taki a duniya inda zai dinga samar da tan miliyan uku a duk shekara.

Kamar yadda ya ce, anyi kashi 48 na aikin matatar kuma daga nan Najeriya za ta zama kasar da ta fi kowacce fitar da kayayyakin man fetur a Afirka.

Ya ce: "Daya daga cikin dalilan da yasa babban bankin Najeriya ke tallafa mana shine, a duk lokacin da muka fara aiki zamu rage yawan marasa aikin yi kuma zamu rage yawan fitar da danyen man fetur da ake yi.

"Zamu kasance daya daga cikin kasashen da ke daga kamfanoni a duniya. Zan iya cewa idan ba taimakon gwamnati, babu inda zamu kai."

Ya kara da cewa, "Dole mu mika godiya ga Shugaban kasa a kan sabbin tsare-tsarensa. Ina godiya ga gwamnan babban bankin Najeriya da ya kawo tsarin raguwar ruwa a bashi wanda hakan ke matukar kara wa 'yan kasuwa kaimi. Ba zamu jira masu zuba hannayen jari daga kasashen waje ba. Don haka da kanmu zamu dauka matakin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel