Bahallatsar kwangilar sayo makamai: Rabiu Kwankwaso ya wanke Abba da Ganduje

Bahallatsar kwangilar sayo makamai: Rabiu Kwankwaso ya wanke Abba da Ganduje

Tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bara game da zargin da ake yi masa da hannu cikin badakalar kudin makamai a zamanin da yake minista, sa’annan ya wanke manyan hadimansa guda biyu, Injiniya Abba Kabir Yusuf da Abdullahi Umar Ganduje.

A makon nan ne wasu rahotanni daga jaridu daban daban suka bayyana cewa hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kaddamar da bincike a kan badakalar kwangilar sayo makamai da aka yi a ma’aikatar tsaro a shekarar 2008.

KU KARANTA: Buhari ya yi magana game da kisan gillar da yan bindiga suka yi a Kaduna

Sai dai jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Kwankwaso ya kasance ministan tsaro ne daga shekarar 2003 zuwa shekarar 2006, kamar yadda tsohon gwamnan ya tabbatar da kansa.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun babban sakatarensa, Muhammadu Inuwa Ali, tshon gwamnan Kano ya musanta rahotannin, inda ya bayyana cewa ba shi bane minista a lokacin da ake zargin an gudanar da wannan badakala.

“Haka nan ba za mu damu da mayar da martani game da rahotanni marasa tushe dake yawo a kafafen sadarwar zamani da jaridu ba wanda mun san an kitsa su ne kawai don bata ma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suna, amma ganin yadda wasu manyan jaridu suka wallafa rahoton ya zama wajibi mu yi raddi.

“Zargin da ake na cewa ana binciken Rabiu Kwankwaso da hadimansa biyu a lokacin da yake ministan tsaro Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kuma Abba Kabir Yusuf, a kan zargin badakalar kwangila a ma’aikatar tsaro ba gaskiya bane.

“Wata jarida ta ce Abba Yusuf da Abdullahi Ganduje sun amshi naira miliyan 30 da miliyan 50, wannan ba gaskiya bane, don haka muke son mu bayyana ma jama’a gaskiyar cewa a lokacin da ake zargin an yi badakalar, watau shekarar 2007, ba Kwankwaso bane ministan tsaro.

“Kwankwaso ya yi murabus a watan Nuwambar 2006 domin ya samu daman tsayawa takarar gwamnan jahar Kano, a wannan lokaci mukami daya kawai yake rike da shi shi ne wakilin Arewa maso yamma a kwamitin gudanarwa na hukumar kula da yankin Neja Delta, inda a shekarar 2010 ya yi murabus da kansa sakamakon yadda ake tafka rashawa a hukumar.” Inji shi.

Kwankwaso ya cigaba da bayyana cewa a wannan lokacin, Ganduje na Ndajema a matsayin babban sakataren hukumar tafkin Chadi, don haka babu yadda za’a yi a ce wai Kwankwaso ko wani hadiminsa suna da hannu a cikin badakalar kwangilar da ake zargin an yi a wannan lokaci.

“Don haka muke kira ga manyan gidajen jaridu da kafafen watsa labaru su kauce ma wallafa labarun da basu da tushe balle makama wanda ka iya bata sunan mutanen da ake zargin, da kuma kamfanonin jaridun kansu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel