Jerin bayanai 11 da ba su inganta ba dangane da cutar Coronavirus

Jerin bayanai 11 da ba su inganta ba dangane da cutar Coronavirus

A yayin da aka fara yakin dakatar da da wanzuwar annobar cutar Coronavirus a Najeriya tun bayan bullarta ta hannun wani mutumin dan kasar Italiya a ranar Juma’a, hukumomi sun tashi haikan wajen ilimantar da jama’a game da cutar.

Majalisar dinkin duniya ta kawo wasu karairayi guda 11 da ake yayatawa game da cutar Corona virus wanda shaci fadi ne kadai, ba su madogara daga binciken kimiyya ko masana, don haka basu da tushe balle makama.

KU KARANTA: Za’a tura tubabbun mayakan Boko Haram jami’o’in kasashen waje don yin karatu

Jerin bayanai 11 da ba su inganta ba dangane da cutar Coronavirus
Jerin bayanai 11 da ba su inganta ba dangane da cutar Coronavirus
Asali: Facebook

1- Cewa wai na’urar busar da hannu (Hand dryers) na da kashe kwayar cutar Coronavirus

2- Cewa wai hasken fitilun na’urorin bincike (Thermal scanners) na gano masu cutar Coronavirus

3- Cewa wai ruwan giya ko sinadari Chlorine na kashe kwayar cutar Coronavirus a jikin dan Adam

4- Cewa wai kada a sake amsan sakonni kayayyaki daga kasar China, don gudun kamuwa

5- Cewa wai dabbobin gida suna harba cutar Corona virus, shi ma karya ne.

6- Cewa wai allurar rigakafin ciwon sanyi nimoniya kariya ne daga kamuwa da Coronavirus

7- Cewa wai hanci da ruwan gishiri na bayar da kariya daga Corona virus

8- Cewa wai cin tafarnuwa na hana kamuwa da cutar Coronavirus

9- Cewa wai man ridi na kashe kwayar cutar Coronavirus

10- Cewa wai Coronavirus matasa kawai yake kamawa, a’a, kowa da kowa na iya kamuwa

11- Cewa wai an samu maganin dake warkar da cutar, a’a, har yanzu ba’a gano ba maganinta ba.

Ita dai wannan cuta da aka fara samunta daga birnin Wuhan na kasar China tana shafar numfashin dan Adam ne, kuma zuwa yanzu sama da mutane 80,000 sun kamu yayin da akalla mutane 2,000 suka mutu, yawancinsu a kasar China.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel