Hukumar kare haddura ta haramta zaman fasinja 2 a gaban motar haya

Hukumar kare haddura ta haramta zaman fasinja 2 a gaban motar haya

Hukumar kiyaye haddura ta kasa, FRSC, ta nanata matsayinta na haramta dauka ko zaman fasinjoji guda biyu a gaban motocin haya a dukkanin fadin kasar nan, kamar yadda wani babban jami’in hukumar ya tabbatar.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shugaban sashin wayar da kawunan jama’a na hukumar, Bisi Kazeem ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a.

KU KARANTA: Za’a tura tubabbun mayakan Boko Haram jami’o’in kasashen waje don yin karatu

Hukumar kare haddura ta haramta zaman fasinja 2 a gaban motar haya
Shugaban FRSC
Asali: Facebook

Kazeem ya ce FRSC za ta cigaba da aiwatar da wannan doka ba tare da kakkautawa ba, domin kuwa ba za ta yi kasa a gwiwa a aikinta na tabbatar da lafiyar matafiya a kowanne lokaci ba.

A cewarsa, dokar ta bayyana karara game da laifin daukan kayan da suka wuce gona da iri a ababen hawa, kuma hukumar na cigaba da tabbatar da yan Najeriya sun bi dukkanin dokokin kan hanya.

“Muna kama mutane a kullum, amma abin da ya kamata ku sani shi ne yawancin masu karya wannan doka sun san inda ake kamawa, don haka suke kauce ma bin duk hanyoyin da jami’anmu suke tsayawa.

“Amma a yanzu mun shirya tsaf don shawo kan kalubalen kamar yadda muka saba yi ma game da sauran kalubalai da suka zama karfe kafa ga tsaron hanyoyin mu.” Inji shi.

Game da matsalar sata tare da garkuwa da mutane kuwa, FRSC ta bayyana tabbatar da kokarin da take yin a samar da bayanan sirri ga hukumomin tsaro game da ayyukan miyagu a duk inda suke aiki, inda yace sai da hadin kai da taimakon juna za’a iya shawo kan matsalar.

A wani labarin kuma, A kokarinsa na tabbatar da dokar bayar da ilimi kyauta kuma ilimi dole a jahar Kano, gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya haramta duk wani almajiri yin barace barace a kan titunan jahar.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata, 25 ga watan Feburairu yayin taron mika takardun shaidar daukar aiki ga malamai yan sa kai guda 7,500 da gwamnatin ta dauka don koyarwa a makarantun firamarin jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel