A halin yanzu Iyalaina sun barbazu a gidajen yan uwana suna rabe rabe – Buba Galadima

A halin yanzu Iyalaina sun barbazu a gidajen yan uwana suna rabe rabe – Buba Galadima

Tsohon aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda a yanzu ya rikide ya zama babban dan adawar gwamnatin Buhari, Alhaji Buba Galadima ya bayyana cewa a yanzu haka ya tura iyalansa zuwa gidajen yan uwa tun bayan kwace gidajensa da gwamnatin Najeriya ta yi.

Idan za’a tuna hukumar kula da kadarorin gwamnatin Najeriya ce ta kwace wasu kadarorin Buba da suka hada da gidaje guda biyu da kamfaninsa mai suna Bedko biyo bayan zarginsa da rashin biyan bashin naira miliyan 900 da tace ya karba daga bankin Unity Bank.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta bayyana dalilin da yasa Boko Haram ke kai ma kiristoci hari

Sai dai Buba Galadima ya musanta wannan zargi, inda yace bita da kulli ne kawai ake masa don haka yayi barazanar kwanciya a waje a kofar gidansa dake unguwar Wuse II na babban birnin tarayya Abuja don nuna ma yan Najeriya mawuyacin halin da yake ciki.

Amma a cikin wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust, Buba Galadima wanda ya bayyana cewa a yanzu haka yana jahar Legas a kan maganar, yace iyalansa da yaransa da jikokinsa sun koma gidajen yan uwansa da zama.

“Sun mamaye gidan, kuma iyalaina sun barbazu a wurare daban daban wurin yan uwa. Ni kuma ina Legas don ganin lauyoyin da zasu dauki gabaran tsaya min a kan batun da sauran batutuwa.” Inji Galadima.

Sai dai Buba ya shaida ma majiyar Legit.ng cewa da fari ya so ya nuna tirjiya a lokacin da Yansanda 30 suka diran ma gidan nasa, amma daga bisani ya hakura, amma a yanzu Yansanda sun ragu zuwa 6, bugu da kari ya ce Yansandan suna da kirki.

A wani labarin kuma, gwamnatin Najeriya ta bayyana dalilin da yasa kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta karkatar da hare harenta ga mabiya addinin kiristanci a Najeriya,

Ministan watsa labaru da al’adun Najeriya, Alhali Lai Mohammed ne ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba.

A cewar minista Lai, mayakan ta’addancin Boko Haram suna kai ma kiristoci hari ne domin su kunna rikicin addini a tsakanin mabiya mabanbanta addinai daban daban a Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel