Har zuwa yanzu ba’a gano maganin annobar Coronavirus ba - Hukumar WHO

Har zuwa yanzu ba’a gano maganin annobar Coronavirus ba - Hukumar WHO

Hukumar kiwon lafiya ta majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa har yanzu babu wani takamaimen maganin cutar Coronavirus ko kuma wand aka iya zama riga kafi a gareshi, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar ta bayyana a cikin wata mujallarta na kiwon lafiya cewa allurorin rigakafi da ake amfani dasu don maganin numoniya ciwon sanyi da sauransu ba su bayar da kariya ga cutar Coronavirus.

KU KARANTA: Badakalar satar naira biliyan 2: Abdulrashid Maina na barazanar kashe direbobinsa

Har zuwa yanzu ba’a gano maganin annobar Coronavirus ba - Hukumar WHO
Har zuwa yanzu ba’a gano maganin annobar Coronavirus ba - Hukumar WHO
Asali: UGC

Don haka WHO ta ce cutar Coronavirus cuta ce sabuwa mai zaman kanta, wanda ke bukatar maganinta na daban, amma ta tabbatar da cewa masana na cigaba da gudanar da bincike don samo allurar da zata magance shi.

Ko da yake babu maganin, amma WHO ta yi kira da a bayar da kulawa ta musamman ga mutanen da suka kamu da cutar Coronavirus don warkar da alamominsa, sa’annan ta ce tana bayar da gudunmuwa ga masana dake gudanar da bincike don a gaggauta samar da maganin.

A wani labarin kuma, Masarautar kasar Saudiyya ta dakatar da shiga biranen Makkah da Madina da sunan aikin Umrah sakamakon cigaba da yaduwar annobar cutar Coronavirus da ake samu a kasashen duniya.

Wannan cuta da aka fara samunta daga birnin Wuhan na kasar China tana shafar numfashin dan Adam ne, kuma zuwa yanzu sama da mutane 80,000 sun kamu yayin da akalla mutane 2,000 suka mutu, yawancinsu a kasar China.

Ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje ta kasar Saudiyya ce ta sanar da hana shiga kasar ga baki, musamman daga kasashen da aka tabbatar da samuwar cutar Coronavirus a cikinsu.

A yanzu haka kasashe irinsu Iraqi, Kuwair da Bahrain sun haramta gudanar da duk wani taro da zai tara jama’a tun bayan samun rahoton bullatar annobar Coronavirus a cikinsu, haka zalika sun garkame makarantu da wuraren shakatawa don hana yaduwar cutar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel