Tsaro: Mamba a majalisar wakilai daga jihar Borno ya yi barazanar yin murabus

Tsaro: Mamba a majalisar wakilai daga jihar Borno ya yi barazanar yin murabus

Wani dan majalisar wakilai daga jihar Borno, Ahmadu Jaha yayi barazanar yin murabus saboda rashin tsaron da ya addabi yankin Arewa maso gabas. A yayin zaman majalisar a ranar Talata, yayi barazanar yin murabus din ne tare da zargar sojin kasar nan da yin sansanin kare kansu, kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Kamar yadda ya ce, hakan na sa mayakan Boko Haram din su yi ta harar farar hula.

Jaha ya kara da cewa sojojin na zaune ne kawai a sansanin, inda suke korar 'yan ta'adda a maimakon yakarsu.

Dan majalisar ya jaddada bukatar sallamar shugabannin tsaron kasar nan.

Tsaro: Dan majalisar wakilai yayi barazanar yin murabus
Tsaro: Dan majalisar wakilai yayi barazanar yin murabus
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari ya shiga ganawa ta musamman da shugabannin hukumomin tsaro, babu Monguno (Hotuna)

A wani rahoto na daban, rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta ce ta ki bude wa mayakan kungiyar Boko Haram wuta yayin harin da suka kai garin Garkinda na karamar hukumar a Gombia jihar Adamawa saboda gudun kashe fararen hula marasa laifi.

Mazauna garin sun zargi dakarun rundunar sojin sama da kin kawo musu agaji yayin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari garin a makon da ya gabata.

Da ya ke mayar da martani a kan zargin, Ibikunle Daramola, kakakin rundunar NAF, ya ce akwai karin bayani a kan dalilin da yasa basu bude wa mayakan wuta ko sakar musu bama bamai ba.

Ya ce ba za a zargi rundunar NAF da nuna sakaci wajen tura jiragenta zuwa wurin da aka kai harin ba bayan samun rahoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel