Zargin damfara: Kotu ta bada umarnin damko manajan NIMC

Zargin damfara: Kotu ta bada umarnin damko manajan NIMC

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta ba da umarnin damko manajan hukumar yin katin dan kasa, NIMC, Jamila Muhammad, sakamakon kin bayyana da tayi gaban kotu a kan zarginta da ake da rashawa.

Kamar yadda mai magana da yawun hukumar yaki da almundahanar kudade ta ICPC, Rasheedat Okoduwa ta bayyana, ta ce manajar NIMC din da tsohon daraktan hukumar tsaro da musaya, Mounir Gwarzo, ana zarginsu a kan damfarar wata kwangila ta N12.8m.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, takardar ta ce, "Gwarzo na fuskantar laifuka shida da suka hada da amfani da kujerarsa ba ta yadda ta dace ba da kuma ba wani kamfani mai suna Outbound Investment Limited kwangiloli. Shi ne kuma daraktan kamfanin ko a lokacin da yake babban daraktan SEC.

"A bangaren Jamila Muhammad kuwa, a matsayinta na daraktan Outlook Communication Limited, tana fuskantar laifuka takwas ne da suka hada da mallaka tare da gudanar da aiyukan wani kamfani mai zaman kansa ko a lokacin da take ma'aikaciyar gwamnatin tarayya. SEC ta ba kamfaninta kwangilar N4,372,080."

Zargin damfara: Kotu ta bada umarnin damko manajan NIMC
Zargin damfara: Kotu ta bada umarnin damko manajan NIMC
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Nan da makonni kadan Boko Haram zasu zama tarihi - Buhari

Hukumar ta ce ayyukansu sun ci karo da sashi na 12 da 19 na dokokin hukumar ICPC din na 2000 kuma abin hukuntawa ne.

ICPC ta kara da cewa, an yanke ranar gurfanar da mutane biyun a 18 ga watan Fabrairun 2020 a gaban Mai shari'a O. A. Adeniyi, amma sai Jamila ba ta bayyana gaban kotun ba. Ta ce tana kwance ne a asibitin kasa da ke Abuja.

Lauyan ICPC, George Lawal ya bukaci kotun da ta yarje musu damko wadanda ake zargin don babu wani rahoton likita da ke nuna sahihancin zancen.

Mai shari'a Adeniyi ya bada umarnin a damko Jamila Muhammad kuma ICPC su adanata a ma'adanar masu laifi, yayin da ya dage sauraron shari'ar zuwa 5 ga watan Maris na 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: