Tsuguni bata kare ba: Orji Uzor Kalu na fuskantar sabuwar barazana yayin da yake garkame

Tsuguni bata kare ba: Orji Uzor Kalu na fuskantar sabuwar barazana yayin da yake garkame

- Duk da cewa Orji Uzor Kalu yana gidan gyaran hali a kan zarginsa da ake da rashawa yayin da yake gwamnan jihar Abia, tsuguni bata kare ba

- Mazabar Sanatan sun fara kokarin kwace kujerarsa ta majalisar dattijai tunda basu samun isasshen wakilcin da ya kamata

- Wani dan siyasa, Chief Charles Ike ya bukaci majalisar dattijan da ta bada damar maye gurbinsa da wani

Duk da daure tsohon gwamnan jihar Abia da aka yi a gidan gyaran hali da aka yi sakamakon zarginsa da ake da rashawa, akwai yuwuwar wani kalubale ya sake tunkaro shi.

A halin yanzu wani da siyasa daga jam’iyyar PDP a jihar Abia din na bukatar majalisar dattijan da ta kwace kujerar sanatan.

Kalu, dan majalisar dattijai ne wanda ya tafi gidan gyaran hali tun a 2019 sakamakon hukuncin da kotu ta yanke masa bayan kama shi da tayi da laifin rashawa.

Jaridar The Nation ta bayyana cewa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya dauko rahoto daga Umuahia, babban birnin jihar Abia din a ranar Asabar, 22 Fabrairu.

Tsuguni bata kare ba: Orji Uzor Kalu na fuskantar sabuwar barazana yayin da yake garkame
Tsuguni bata kare ba: Orji Uzor Kalu na fuskantar sabuwar barazana yayin da yake garkame
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Shagalin bikin Laolu Osinbajo, dan mataimakin shugaban kasa (Hotuna)

Ya bayyana cewa, a yayin da Kalu ke gidan gyaran hali, mazabarsa na zaune ne cikin duhu yayin da sauran mazabun jihar ke samun wakilci nagari a majalisar dattijan.

Ya kara da bayyana cewa, mazabar na shirin kiran kalu gida don ba wani damar hayewa kujerarsa ta majalisar dattijan.

Legit.ng ta ruwaito cewa, David Omuoha Bourdex, daya daga cikin ‘yan kwamitin amintattun jam’iyyar APGA yayi kira ga majalisar dattijan da kada ta bada damar maye gurbin kujerar Kalu din yayin da yake gidan gyaran hali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel