Babbar magana: Yadda na sha artabu da gawar abokina - Cewar wani mutumi

Babbar magana: Yadda na sha artabu da gawar abokina - Cewar wani mutumi

- Wani ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ya wallafa yadda ya ci karo da wani abokin shi da ya rasu a Onitsha

- Ya bayyana yadda suka ci karo da abokin nashi kuma ya bashi Sarkar zinari ta $4,000 don ya siyar mishi

- Bayan ya siyar din ne ya tuntubi ‘yan uwanshi da suka tabbatar da cewa dan uwansu ya dade da rasuwa kuma fatalwar shi ce yaci karo da ita

Jaridar Gistmania ta ruwaito yadda wani mutum ya wallafa labarin yadda ya ci karo da fatalwar abokin shi da ya rasu a Onitsha, jihar Anambra. Kamar yadda ya ce, marigayin abokin nashi ya bashi sarka ta $4,000 ya siyar mishi kuma zai dawo ya karba kudin. Bayan dadewar da yayi bai ganshi ba kuma bai ji daga gareshi ba, sai ya tuntubi ‘yan uwan shi wadanda suka tabbatar da cewa ya rasu.

Ga abinda mutumin ya wallafa a kafar sada zumuntar ta zamani:

“Na ga wani abokina a ranar 17 ga watan Fabrairu 2020 na hadu da shi a Onitsha. Duk da ina kallon shi nasan yana da damuwa. Sai ya dauko wata sarkar zinari ya ce gashi nan in taimaka mishi in siyar da ita. Yana so ya karasa ginin mahaifiyarshi ne kafin ruwa ya sauka.

“Nace mishi mu shiga kasuwa tare amma sai ya ce a’a, ya yadda dani. In siyar kawai sai in neme shi. Na bukaci lambar wayar shi amma sai yace sai ya isa Awka sannan zai samu waya, yanzu babu ita tare da shi.

KU KARANTA: Ladanin Masallacin Landan da aka kai wa hari da wuka yace ya yafe duniya da lahira

“A take muka shiga wani shago na samu takarda na rubuta mishi lambar wayata nace ya tuntubeni don jin yadda aka siya. Ya ce ya siyeta $4,000 ne. Daga nan ya tafi ban kara ji daga gareshi ba. Bayan na samu mai siye ne na dinga nemanshi amma na rasa shi.”

Ya ci gaba da cewa, “Daga nan na tuntubi ‘yan uwanshi wadanda suka ce ya mutu tun a watan Janairu. Na samu wata kanwar mahaifiyarshi wacce muka je inda aka siya zinaren na damka mata kudin kacokan. A cewarta dama ya kammala ginin mahaifiyarshi amma a linta kawai ya tsaya. Yanzu zasu yi amfani da kudin don karasawa sannan a birneshi a watan Maris.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel