Mata 5 sun hadu sun kashe dan uwansu da duka saboda ya nemi kaso a sadakin daya daga cikinsu

Mata 5 sun hadu sun kashe dan uwansu da duka saboda ya nemi kaso a sadakin daya daga cikinsu

- Wasu 'yan uwa mata biyar sun lakadawa dan uwansu namiji mugun dukan da yayi sanadin mutuwar shi

- Kamar yadda suka bayyana, ya bukaci a bashi kason shi ne daga cikin sadakin daya daga cikinsu wacce za ta yi aure

- Sun bayyana mamakinsu sakamakon mutuwar shi, don sun ce zatonsu fushi yasa har yayi bacci a dakin mahaifiyarshi

Yan uwa biyar mata sun shiga hannun jami'an tsaro kuma an gurfanar dasu a gaban kotu a ranar Lahadi, 16 ga watan Fabrairu. Ana zarginsu da yi wa dan uwansu namiji mugun dukan da yayi sanadin mutuwar shi bayan ya bukaci wani kaso daga cikin sadakin daya daga cikinsu.

Kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito, Paul Njeri mai shekaru 51 ya sheka lahira ne a yayin da ake shirin bada sadakin daya daga cikin 'yan uwan shi mata a kauyen Mwimuto da ke yankin Kiambu a kasar Kenya.

Mamacin ya jaddada cewa sai an bashi kason shi daga cikin sadakin daya daga cikin 'yan uwanshi. Matan sun duke shi da itace ne. Sun hada da Mary Muthoni, Elizabeth Wairimu, Catherine Wanja, Alibera Njambi da Susan Wambui.

KU KARANTA: Tirkashi: Direban fitaccen dan luwadin nan Bobrisky ya arce masa da mota da kudi rabin miliyan a ciki

Shugaban 'yan sandan yankin arewacin Gatundu, Steve Kirui ya tabbatar da cewa an kama wadanda ake zargin. Sun sha mamakin mutuwar dan uwan nasu don kuwa sun ce zatonsu bacci yayi bayan ya kulle kanshi a dakin mahaifiyarsu.

Kirui ya ce, "An fara shagali ne kafin a biya sadakin. Wadanda ake zargin kuwa sun hada kai ne inda suka lakada wa mamacin duka bayan ya bukaci a bashi wani kaso na sadakin."

An gurfanar dasu a ranar Litinin, 17 ga watan Fabrairu yayin da aka mika gawar shi babban asibitin Kago. Za a fara binciken sanadin mutuwar shi a ranar 19 ga watan Fabrairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel