Gwamnati za ta fuskanci bore daga matasa saboda rashin biyan albashin N-Power

Gwamnati za ta fuskanci bore daga matasa saboda rashin biyan albashin N-Power

Matasa yan Najeriya dake cikin gajiyar tsarin bayar da tallafi na N-Power sun yi barazanar shiga yajin aiki na dindindin tare da gudanar da gangamin zanga zangar nuna bacin ransu bisa yadda gwamnati ta gaza biyansu albashin watan Janairu.

Sahara Reporters ta ruwaito matsalar rashin samu hakkokin yan N-Power ba sabon abu bane tun bayan zuwa sabuwar ministar shugaban kasa Buhari, Sa’adiya Umar Faruk, inda aka dauke N-Power daga ofishin shugaban kasa ya koma karkashin ma’aikatarta.

KU KARANTA: Cigaban ilimi: BUK ta kaddamar da gidan talabijin da rediyo a jahar Kano

Ko a watan Oktobar 2019 ma sai da matasan suka koka sakamakon daukan watanni uku kafin nan suka samu kudadensu, wanda hakan yasa yan Najeriya ke ganin kamar akwai wata makarkashiya da ministar ke yi na ganin ta dakile shirin, a cewar majiyarmu.

Matasan na N-Power a karkashin wata kungiya mai suna National Association of Npower Volunteers sun bayyana cewa za su shiga yajin aiki idan har ba’a biyasu hakkokinsu ba, haka nan sun nemi minista Sadiya ta yi murabus saboda tsaiko da ake samu wajen biyansu hakkokin nasu.

“Muna ganin Hajiya Faruk tana da wani manufa na yin zagon kasa ga tsarin gwamnatin tarayya na taimaka ma matasa tare da kawar da rashin aikin yi a tsakaninsu saboda ta cigaba da rike kudaden jama’a babu gaira babu dalili.

“Don haka muke kira ga ministar ta fada mana dalilinta na kin biyanmu hakkokinmu, musamman bayan mun bata lokacinmu da karfin har ma kudinmu wajen yi ma gwamnatin tarayya aiki, haka zalika muna bukatar jin dalilinta na cigaba da rike wannan mukami idan ta san ya fi karfinta.

“Saboda yawancin rayuwar matasanmu ya dogara ne ga wannan kudin da take cigaba da rikewa, saboda haka zamu gudanar da zanga zangar nuna bacin rai da ita a fili da kuma yanar gizo don bukatar ta yi murabus, kuma a biyamu kudinmu.” Inji kungiyar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: