Ta’addanci: Boko Haram ta kashe malaman makaranta 547 a yankin Arewa maso gabas

Ta’addanci: Boko Haram ta kashe malaman makaranta 547 a yankin Arewa maso gabas

Kungiyar malamai ta Najeriya, NUT, ta bayyana kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta kashe akalla malaman makarantu guda 547 tun bayan barkewar rikicin ta’addanci a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Premium Times ta ruwaito shugaban kungiyar, Nasir Idris ne ya bayyana haka a ranar Talata a babban birnin tarayya Abuja yayin wani taron kungiyar, inda yace har yanzu gwamnati ba ta biya iyalan mamatan hakkokinsu ba.

KU KARANTA: Za’a shiga wahalar mai a Kano, Katsina da Jigawa dalilin yajin aikin direbobin tanka

“Abin takaici ne daga cikin iyalan mamatan akwai yara dake karatu a manyan makarantu, amma a sakamakon rashin iyayensu dole suka daina zuwa makaranta, wasu kuma basa ko iya zuwa wajen aiki.” Inji shi.

Amma shugaba Nasir yace kungiyarsu za ta cigaba da tuntubar gwamnatocin jahohin Arewa maso gabas domin tabbatar da ganin sun biya iyalan malaman hakkokinsu. Haka zalika Nasir ya bayyana tattaunawar da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari game da kara wa’adin shekarun ritaya na Malamai zuwa 65.

“Shugaban kasa ya bukaci mu aika bukatunmu game da karin yawan shekarun malamai a rubuce ga ministan ilimi. Kuma zuwa yanzu muna samun nasara, mun tsallake matakai da dama, tun daga majalisar dattawa, majalisar wakilai, dukkansu sun amince da bukatarmu.

“Muna ganin akwai bukatar tun da dai an kara ma malaman jami’o’i shekarun ritaya zuwa 65, su ma malaman sakandari da firamari ya kamata su mori wannan tsari.” Inji shi.

Daga karshe shugaban NUT ya bayyana cewa gwamnatoci basa daukan malamai aiki a yankunan karkara wanda hakan kuma ya samar da gibi a fannin ilimi, shi yasa suke neman a kara shekarun ritaya don malamai su dade suna aikinsu na koyarwa.

A wani labarin kuma, Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya tabbatar da samun rahoton barazanar kai ma majalisar dokokin Najeriya hari da wasu miyagun yan ta’adda suke shirin kaiwa.

Lawan ya koka ne a ranar Talata, 18 ga watan Feburairu, yayin ganawa da shuwagabannin tsaro, inda yace mutane da dama da ba’a san ko su wanene ba, suna shige da fice a majalisar ba tare da samun takardar gayyata ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel