Tirkashi: Uba ya bindige dan shi har barzahu, bayan ya gano cewa kasurgumin dan luwadi ne

Tirkashi: Uba ya bindige dan shi har barzahu, bayan ya gano cewa kasurgumin dan luwadi ne

- A lokacin da wasu kasashe na duniya suke ganin cewa lokaci yayi da ya kamata a bawa mutane damar yin auren jinsi, ciki kuwa harda kasar Amurka

- Sai gashi wani mutumi wanda yake zaune a kasar ta Amurka tare da iyalanshi ya harbe dan shi har lahira bayan ya gano cewa kasurgumin dan luwadi ne

- An bayyana cewa mutumin dama ya sha gwada dan nashi da bindiga a duk lokacin da ya kama shi da wani namiji a irin wannan hali

Jami’an hukumar ‘yan sanda sun kama wani mutumi da laifin kashe danshi, bayan ya gano cewa dan nashi ya koma dan luwadi.

Mutumin mai suna Wendell Melton, mai shekaru 53, ya kashe danshi dan shekara 14 mai suna Giovanni Melton, dukan su suna zaune a Henderson, Nevada ne dake kasar Amurka, kamar yadda jami’an ‘yan sanda suka bayyana.

Tirkashi: Uba ya bindige dan shi har barzahu, bayan ya gano cewa kasurgumin dan luwadi ne
Tirkashi: Uba ya bindige dan shi har barzahu, bayan ya gano cewa kasurgumin dan luwadi ne
Asali: Facebook

Lamarin dai ya samo asali ne ranar Alhamis, akan yadda aka yi dan shi yake da saurayi.

Kishiyar mahaifiyar Giovanni, Sonia Jones, ta ce: “Abin yana ci mishi tuwo a kwarya idan ya tuna cewa danshi dan luwadi ne.

“Na tabbata a cikin zuciyar shi yana ji ina ace dan nashi ya mutu ne da ya cigaba da zama da dan luwadi."

Ta bayyana cewa akwai lokacin da Wendell yayi kokarin harbe dan nashi a lokacin da ya kama shi da wani suna iskanci.

“Yan sanda sun zo wajen da lamarin ya faru ranar Alhamis bayan su nsamu rahoton hayani da ke damun mutanen yankin."

KU KARANTA: Tirkashi: Uwa da 'Ya sun haihu a lokaci daya bayan wani ya dirka musu cikin shege

Lokacin da jami’an ‘yan sandan suka iso wajen sun tarar da dan cikin wani yanayi suka yi gaggawar garzayawa dashi asibiti na St Rose Dominican, inda ya mutu a can.

An kama Wendell sannan aka tsare shi, ana tuhumarsa da laifin kisan kai muraran, cin zarafin yaro, da kuma amfani da makami ta hanyar da ba ta dace ba.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata, mun kawo muku labarin yadda shugaban kasar Rasha ya kekasa kasa ya ce mutukar yana raye kuma yana kan mulki babu wanda ya isa yayi auren jinsi a kasar shi.

Wannan lamari bai yiwa mutane da yawa dadi ba a kasar, domin kuwa a lokacin ne wasu kasashe na duniya suke bawa mutane lasisin gabatar da auren na jinsi ga junansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel