Diloli sun bayyana sirrin farin jinin dan tofi da rigar mama na gwanjo

Diloli sun bayyana sirrin farin jinin dan tofi da rigar mama na gwanjo

Masu sana'ar kayan da aka riga aka fara sakawa wadanda ake kira da "Gwanjo" a ranar Talata sun danganta karkon kayan, ballantana kayan ciki na mata da yadda kasuwancin ke ci gaba.

Wadanda suka samu zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai Najeriya (NAN) a wuraren siyar da kayan na jihar Legas, sun ce babu wani dan kamfai, rigar nono da sauran kayan ciki da za a iya kwatanta nagartarsu da gwanjon.

Masu siyarwan sun sanar da kamfanin Dillancin labarai cewa su fa sana'a daram don kuwa yadda ake rige-rigen siya abin alfahari ne.

Kamar yadda Uchechukwu Ndukwe, babban dilan rigunan nono a kasuwar Katanguwa da ke yankin Abule-Egbe a jihar Legas yace, duk da haramta siyar da kayan gwamnjon da gwamnatin tarayya tayi, siyar da kayan gwanjon na daga cikin kasuwanci mai ci a yanzu.

"In har zan sanar da gaskiya, duk da kalubalen da muke fuskanta a kasar nan, mutum na zama dila ne idan ya bude gwanjo mai cike da sabbin kaya ballantan kayan ciki na mata. Wannan na matukar ci don wasu har ajiye kudinsu suke yi idan ya samu," Ndukwe yace.

Diloli sun bayyana sirrin farin jinin dan tofi da rigar mama na gwanjo
Kayan gwanjo
Asali: Facebook

Ya ce ranakun Litinin, Laraba da Juma'a ne ake amfani dasu wajen bude sabuwar dila.

Innocent Uyi wanda ke kasuwar Oshodi ta jihar Legas, ya ce a baya yana siyar da soffi da sabbin kaya amma yanzu ya koma gwanjon don kwastomomi sun fi son su.

DUBA WANNAN: Yawan yi wa miji barazanar kisa da wuka: Kotu ta raba auren mata da miji

"Wasu manyan kwastomomi sun fi son kayan manyan kamfanoni kamarsu Next, Prada, Marks and Spencer da sauransu. Yadda kwastomomi ke son dan kamfai da rigar nono na gwanjo yana kara mana kwarin guiwa," a cewar Uyi.

Wata kwastoma mai suna Precilia Briggs ta sanar da Kamfanin Dillancin Labarai a kasuwar Katanguwa cewa, ta fi son dan kamfai da rigunan nono na gwanjo kuma ba ta kunyar siyansu a kasuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel