Barazanar Shekau: Hukumomin tsaro sun dauki sabbin matakan tsaron Ministan sadarwa

Barazanar Shekau: Hukumomin tsaro sun dauki sabbin matakan tsaron Ministan sadarwa

Gwamnati ta kara adadin jami’an tsaron dake tare da ministan sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami biyo bayan kashedi tare da barazanar kai masa da shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi.

Punch ta ruwaito Shekau ya yi ma Pantami barazana ne biyo bayan bayyana wani sabon dabarar dakile sadarwa a tsakanin mayakan Boko Haram, ashe lamarin ya harzuka Shekau, da wannan yasa ya fitar da sabon bidiyo har ma yana sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Jiragen yakin Najeriya sun yi watsa watsa da sansanin yan Boko Haram a Borno

Sai dai duk da wannan barazana ga rayuwarsa, Minista Pantamiya kai ziyara wata makarantar sakandari ta Garki a ranar Litinin, inda ya koyar da daliban kwalejin darasin kimiyya da fasaha, tare da kira a garesu su rungumi ilimin kimiyya da fasaha.

Shehin Malamin ya dauki tsawon lokaci yana bayar da ilimi g daliban game da muhimmancin ilimin kimiyya da fasaha, musamman ilimin zamani da ya shafi na’urori masu kwakwalwa, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

A yayin ziyarar, an hangi karin jami’an hukumar DSS da na Yansanda sun kakkame a wurare daban daban a ciki a wajen makarantar dauke da makamai suna ta mazurai, duk don tabbatar da tsaron Malamin ministan.

Sai dai koda yan jaridu suka tuntube shi bayan ya kammala koyarwar game da barazanar da Shekau ya masa sai yace: “Ba ni da wani abin da zan ce a yanzu.”

A wani labarin kuma, babban lauya mai zaman kansa, Femi Falana ya bayyana cewa za su shigar da kara gaban kotu domin tilasta ma shugaban kasa Muhammadu Buhari tsige manyan hafsoshin tsaron Najeriya bisa dalilin karewar wa’adinsu.

Falana ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin na Channels, inda yace haramun ne shugaban kasa Buhari ya kara ma hafsoshin tsaron wa’adin mulki, don haka yace sun ci lokacinsu.

Sai dai da aka tambaye shi me yasa ba’a kalubalanci gwamnatin ba idan da gaske yake sai yace: “Ina tabbatar maka cewa a yanzu haka akwai shirin da ake yin a shigar da gwamnati kara game da wannan batu.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel