Allah Sarki: Saurayi ya kashe kanshi, bayan budurwar da ya dauki nauyin karatun ta gaba daya ta fara shirin auren wani saurayi daban

Allah Sarki: Saurayi ya kashe kanshi, bayan budurwar da ya dauki nauyin karatun ta gaba daya ta fara shirin auren wani saurayi daban

- Wani mutum ya yanke shawarar daukar rayuwar shi da kanshi bayan ya samu katin gayyata zuwa bikin budurwarshi

- Ba bakin cikin cin manar da aka mishi bace ta sa ya kashe kanshi, bakin cikin yadda ya dau nauyin karatunta ne har ta kammala jami’a

- Mutumin dai dan asalin jihar Anambra ya samu katin gayyata zuwa bikin da za a yi a ranar 20 ga watan Maris ne ta hannun kawar amarya

Wani mutum ya yanke shawarar kashe kanshi ta hanyar rataya a bishiyar mangwaro bayan da ya gano cewa budurwarsa da ya dau nauyinta ta kammala jami’a na shirin auren wani daban.

Ganau ba jiyau ba, ya ce mummunan lamarin ya faru ne a jihar Anambra. Izuchukwu Ikeli ya kashe kanshi ne bayan da Melisa Nnaji ta kammala karatunta na jami’a da taimakonsa amma za ta angwance da wani daban.

KU KARANTA: Bokan da yake bawa maza maganin mata ya sume bayan ya iske budurwarshi da wani kato suna iskanci

Kamar yadda jaridar Gistmania ta wallafa, “Wannan shine Izuchukwu Ikeli dan asalin Umuleri daga jihar Anambra a Najeriya. Ya kashe kan shi ne ta hanyar rataya a bishiyar mangwaro bayan ya gano cewa budurwar shi za ta auri wani daban. Shi ya dau nauyin Melisa Nnaji har ta kammala karatunta a jami’a. Ta yi mishi alkawarin auren shi bayan ta kammala karatun.”

“Abin bakin cikin shine yadda mutumin ya kasa jure wannan lamarin bayan ya samu katin gayyata zuwa bikin Nnaji da za a yi a ranar 18 ga watan Maris na 2020. Ya samu katin ne ta hannun babbar kawarta mai suna Nnadozie wanda hakan ya kai shi ga kashe kan shi.” Ta kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel