Ritayar Zainab Bulkachuwa a watan Maris na neman kawo rabuwar kai a bangaren Shari'a

Ritayar Zainab Bulkachuwa a watan Maris na neman kawo rabuwar kai a bangaren Shari'a

A yayin da Mai shari’a Zainab Bulkachuwa ke shirin murabus a ranar 6 ga watan Maris yayin da ta cika shekaru 70, akwai shirye-shiryen da wasu ke yi ta bayan fage na wanda zai gajeta a ciki da wajen NJC, kamar yadda jaridar ThisDay ta gano.

Jaridar ta gano cewa duk da wanda zai gajeta din ya kamata ya zama babban mai shari’ar da ke biye da ita a kotun daukaka kara, akwai yunkurin da ake yi don hana mace sake jagorantar kotun. Mai shari’a Monica Dongban-Mensem ita ce biye da Bulkachuwa din da za ta yi murabus.

Mai shari’a Dongban-Mensem diya ce ga mai shari’a M.B Douglas-Mensem. ‘Yar asalin karamar hukumar Shendem ce da ke jihar Filato kuma shi ke shugabantar kotun daukaka kara da ke jihar Filato.

Jaridar ThisDay ta gano cewa ana kokarin tirsasa Mai shari’a Dongben-Mensen da ta amince don komawa kotun koli don ba wa Mai shari’a Mohammed Lawal Garba, wanda ke biye da ita a kotun wuri.

Mai shari’a Garba shi ne mai shugabantar kotun daukaka kara ta jihar Legas kuma shi ya jagoranci shari’ar kotun sauraron kararrakin zabe na 2019.

Ritayar Zainab Bulkachuwa a watan Maris na neman kawo rabuwar kai a bangaren Shari'a
Ritayar Zainab Bulkachuwa a watan Maris na neman kawo rabuwar kai a bangaren Shari'a
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sabbin masarautu: Kotu ta yi watsi da karar masu hannu a nada sabon Sarki

Wannan kotun ce ta jaddada nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019 wanda har aka kai ga kotun koli.

A bangaren Dongban-Mensem, a 2015 ta jagoranci alkalai biyar da suka yi shari’ar kotun daukaka kara ta jihar Ribas wacce ta kwace kujerar Gwamna Nyesom Wike tare da umartar a sake zabe cikin kwanaki 90.

Kamar yadda majiyar ta sanar, an tuntubeta ne don gudun rikicin da ya faru a lokacin da aka mika sunan Mai shari’a Ayo Salami zuwa kotun koli ba tare da saninsa ba.

An gano cewa, matsin da aka yi mata yayi yawa ta yadda aka dinga tuntubar na kusa da ita don su bata shawara ta karba karin girman, amma ta ki.

Jaridar ThisDay ta gano cewa, koda kuwa NJC din da ke son kaita kotun kolin sun hakura, to fa na wajen NJC din basu hakura ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel