Buhari ya aminta da ba masana'antun waka da fim tallafin N7bn

Buhari ya aminta da ba masana'antun waka da fim tallafin N7bn

Ministan kudi, kasafi da tattali, Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya ta hannun BoI ta aminta da fitar da biliyan bakwai don tallafawa masana'antun nishadi. Ahmed ta sanar da hakan ne a taron shekara na Greeners Business to Business da aka yi Abuja a ranar Asabar.

Ta samu wakilcin babban mai bata shawara a kan yada labarai da sadarwa, Armstrong Takang wanda ya ce an amince da wadannan makuden kudin ne don karfafa harkar nishadi.

Ahmed ta ce don tabbatar da gina matasan Najeriya, shirin kirkire-kirkire na N-Power an kawo shi ne don horar da hazikan matasa 5,000 masu nasibi a bangarorin nishadi.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, an yi hakan ne don masana'antar ta zamo za ta iya gogayya da kowacce a duniya.

Buhari ya aminta da ba masana'antun waka da fim tallafin N7bn
Buhari ya aminta da ba masana'antun waka da fim tallafin N7bn
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sauya su Buratai: Fadar shugaban kasa ta bankado shirin masu cin moriyar kungiyar Boko Haram

Ta bayyana cewa wadanda suka amfana din an horar da su ne a bangarori kala-kala. Sun kuma samu kayan aiki ta yadda zasu kware ko bayan horarwar.

A yayin jawabin ministar a kan AFCTA, ta ce manyan bagarorin sun hada da waka, samar da fina-finai da kyale-kyale.

Kamar yadda ta ce a 2016, masana'antar fim ta bada gudumawa N239 biliyan ga kasar nan. Bangaren wakoki kuwa ya bada kashe 9 a 2016.

Ahmed ta bayyana cewa, masana'antar waka kadai ana so ta bada gudumawar kashi 13.4 na jimillar GDP na kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng