Barawo ya sace waya tare da kwashe kudin asusun bankin, ya kara da cin bashin bankin

Barawo ya sace waya tare da kwashe kudin asusun bankin, ya kara da cin bashin bankin

- Rayuwar wani mutum ta shiga garari bayan da barawo ya sace mishi waya a tashar mota ta Ibadan

- Barawon ya kwashe kudin da ke asusun bankin mutumin tare da karawa da karbar bashin banki wanda ya kwashe

- Kamar yadda Benson, dan mutumin ya bayyana, tuni dai an kai korafin ga ‘yan sanda, hukumar EFCC da kuma SSS

Rayuwar wani mutum ta shiga garari bayan da barawo ya dauke mishi waya tare da kwashe mishi kudin asusun bankin shi. Bayan nan, barawon bai tsaya ba sai da ya ci bashin banki ta asusun, kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito.

Wani ma’abocin amfani da kafar sada zumunta mai suna Benson, ya koka da yadda wani barawo ya sace wayar mahaifin shi a tashar mota da ke Ibadan. Barawon ya kwashe kudin asusun bankin mahaifin nashi. Daga nan bai tsaya ba, sai ya kara da karbar bashin bankin ta asusun.

Amma ya bayyana cewa a halin yanzu an garzaya wajen ‘yan sanda, hukumar yaki da rashawa da kuma ‘yan sandan fararen kaya. Wannan al’amarin ya faru ne a ranar Talata, 11 ga watan Fabrairu na 2020.

Barawo ya sace waya tare da kwashe kudin asusun bankinshi, ya kara da cin bashin bankin
Barawo ya sace waya tare da kwashe kudin asusun bankinshi, ya kara da cin bashin bankin
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sirrin dukiya da daukakata ya dogara ne da yawan 'yan matan da nayi lalata dasu - Tsohon golan Najeriya

Kamar yadda ya wallafa, “mahaifina ya shiga wani hali bayan an sace wayar shi a tashar mota a Ibadan a ranar Talata. Barawon ya kwashe kudin asusun bankin shi sannan ya kara da cin bashin banki ta asusun. Na tausayawa barayin idan kuwa suka shiga hannu.”

“A halin yanzu an sanar da ‘yan sanda, hukumar yaki da rashawa ta EFCC da kuma jami’an tsaro na fararen kaya. Ko waye kuwa zai shiga hannu. Gareku jama’a, a dinga adana waya. Mutanen nan basu da tausayi.” Ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel