Kudin makamai: Dasuki ya nemi Kotu ta ba shi izinin tafiya duba lafiyarsa a kasar waje

Kudin makamai: Dasuki ya nemi Kotu ta ba shi izinin tafiya duba lafiyarsa a kasar waje

Wata babbar kotun birnin tarayya Abuja ta sanya ranar 19 ga watan Feburairu domin sauraron bukatar da tsohon mashawarcin tsohon shugaban kasa a kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki ya mika mata yana neman ta ba shi daman ficewa daga kasar nan.

Daily Trust ta ruwaito Dasuki ya nemi kotun ta sakar masa fasfonsa na fita kasar waje ne domin ya samu daman fita zuwa asibitin kasar waje don ya duba lafiyarsa bayan kwashe tsawon shekaru 4 a garkame a kurkuku.

KU KARANTA: Buhari ya yi alkawarin sake gina gidajen da Boko Haram ta kona a Auno tare da biyan fansa

Tun a shekarar 2015 ne aka gurfanar da Dasuki gaban Alkali mai sharia Husseini Baba-Yusuf a kan tuhume tuhume da dama tare da wasu mutane. Alkalin ya sanya wannan rana ne bayan lauyan Dasuki, Adeolu Adedipe ya shaida masa cewa tun a ranar 11 ga watan Feburairu ya sanar da EFCC game da bukatarsu.

Sai dai lauyan EFCC, Adebisi Adeniyi ya bayyana ma kotun cewa tabbas sun samu takardun bukatar Dasuki, amma suna bukatar lokaci domin su gudanar da cikakken nazari cikin natsuwa game da bukatar tasa.

“Babban kalubalen da muke fuskanta a nan shi ne ba mu tabbatar da ko fasfon wanda ake kara yana hannun kotu ba, domin kuwa baya hannun mu masu kara.” Inji shi.

Dasuki na fuskantar tuhuma ne tare da tsohon karamin ministan kudi, Bashir Yuguda, tsohon gwamnan jahar Sakkwato, Attahiru Bafarawa da dansa Sagir Bafarawa da kuma kamfaninsa Dalhatu Investment Limited.

A wani labarin kuma, Babban sufetan Yansandan Najeriya, IGP Muhammad Adamu ya amince da tsarin rundunar tsaro ta yankin Yarbawa, watau Amotekun, bayan gwamnonin jahohin yankin sun rattafa hannu kan tsare tsaren aikin rundunar.

Gwamnonin sun bayyana ma IG Adamu cewa rundunar Amotekun za ta taimaka wajen kare yankin daga ayyukan miyagun mutane, tare da tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyinsu.

Gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu SAN ne ya bayyana haka a madadin gwamnonin yankin kudu maso yammacin Najeriya, a yayin taron tsaro na yan doka da babban sufetan Yansandan ya kira a ranar Alhamis a jahar Legas.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel