Gwamnatin Buhari ta binciko fiye da gangan danyen mai biliyan 1 a Arewa maso gabas

Gwamnatin Buhari ta binciko fiye da gangan danyen mai biliyan 1 a Arewa maso gabas

Karamin ministan man fetir, Timipre Sylva ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gano fiye da gangan danyen mai biliyan daya a kwance a cikin yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Minista Sylva ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru daya gudana a karshen taron man fetir na kasa da kasa da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 12 ga watan Feburairu.

KU KARANTA: Magidanci ya lakada ma matarsa dan banzan duka har sai da ta ce ‘ga garinku’

“Daga sakamakon da muke samu, duk da dai alkalumman basu gama fitowa ba, amma bincike ya nuna akwai fiye da gangan danyen mai biliyan 1 a kwance a yankin Arewa maso gabas, kuma mun fara fahimtar yadda yanayin kasar wurin take.” Inji shi.

Ministan yace har yanzu Najeriya ba ta kammala gano iya arzikin man ta ba, don haka yace akwai bukatar cigaba da gudanar da binciken neman danyen man fetir a sassan kasar nan domin gano sauran arzikin man.

Game da kammala aiki a kan dokar masana’antar man fetir kuwa, Sylva yace suna sa ran majalisa za ta gama aiki a kan dokar zuwa watan Yunin shekarar 2020, ya kara da cewa akwai bukatar rattafa hannu a kan dokar domin janyo masu zuba hannun jari.

Haka zalika ministan yace a cikin watanni uku na farkon shekarar 2020 za’a fara aikin gyara matatar mai ta Fatakwal. “Za mu fara aikin gyaran matatun mai daga matatar mai ta Fatakwal saboda muhimmancinsa, idan har muka iya kammala aikin fatakwal, zamu cimma gagarumar nasara.

“Amma muna cigaba da gudanar da nazari game da matatun main a Warri da na Kaduna.” Kamar yadda kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shi.

A wani labarin kuma, babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa bai kamata a tunzura shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen daukan matakin tsige manyan hafsoshin tsaro ba, saboda shi kadai ya san inda matsalar take.

A kwanakin baya ne majalisar dokokin Najeriya ta nemi Buhari ya sallamki kafatanin hafsoshin tsaron Najeriya saboda abin da suka bayyana a matsayin gazawarsu wajen kare rayukan yan Najeriya, duba da sake farfadowar da Boko Haram ta yi.

Da wannan ne babban hafsan Sojan, Laftanar Janar Tukuru Tusuf Buratai yace: “Ba tare da kalubalantar ikon majalisa ba, amma sallamar hafsoshin tsaro ba shi bane hanyar da zai warware matsalolin tsaro da Najeriya ke fama da ita.”

Buratai ya kara da cewa Buhari na sane da halin da ake ciki, kuma shi ne mai dakin, shi ya san inda ke masa yoyo, haka zalika shi kadai ne zai iya yanke hukuncin da ya kamata game da lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel