Daukar doka a hannu: An kone wani mutumi kurmus akan ya saci zakara

Daukar doka a hannu: An kone wani mutumi kurmus akan ya saci zakara

- Wani mutum mai matsakaicin shekaru ya hadu da ajalin shi bayan da ya saci zakara su kuwa jama’a suka banka mishi wuta

- Mamacin ya dade yana irin wannan halin na dauke-dauke kamar su janareto, batiri, kaji da sauransu a yankin

- A ranar da ajali ya kira shi, ya fita da sassafe ne inda ya je satar kaji amma sai jama’ar yankin suka farga tare da kone shi

Wani mutum mai matsakaicin shekaru da ya saci kaza ya hadu da ajalinshi. An zargi mutumin ne da satar kazar a titin Ekpo Edem da ke karamar hukumar Calabar ta Kudu a jihar Cross River. Jama’ar yankin ne suka fusata inda suka taru tare da banka mishi wauta bayan an kama shi.

Mamacin wanda aka gano sunan shi da Victor, ya kone kurmus a sa’o’in farko na ranar Talata, 10 ga watan Fabrairu 2020. An zarge shi da kwarewa a wajen satar abubuwa kanana kafin mutuwar shi a yankin, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Wani ganau ba jiyau ba mai suna George Asuquo ya sanar da jaridar Vanguard cewa:

“Wanda aka kone din ya saba satar kananan abubuwa irinsu batiri, janareto da kuma dabbobin da suka hada da kaji a yankin. Amma kuma jama’a sun gane shi sosai.

“Bai taba sani cewa mutane sun gano mugun halin shi na sata kamar bera. Duk da cewa an kama shi a watan da ya gabata kuma an ja mishi kunne, hakan na nuna cewa bai ji maganar ba.

KU KARANTA: Ramuwar Gayya: Budurwa ta kira babbar kawarta a waya a lokacin da take lalata da mahaifinta, bayan kawar ta kwace mata saurayi

“Kamar dai yadda ya saba, ya fito da sassafe a ranar Talata don satar kaji amma sai kaji suka fara kuka har jama’a suka ji. Ba a jinkirta ba kuwa aka kama dukan shi tare da banka mishi wuta inda ya kone kurmus.”

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, ASP Irene Ugbo ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta nuna tsananin damuwar ta a kan wannan aika-aikar.

Ta ce: “Ba ma goyon bayan masu laifi ko masu laifi. Amma dole ne mutane su gane cewa bai kamata su dau hukunci a hannunsu ba. Su mika wadanda ake zargi hannun jami’an tsaro don ci gaba da bincike tare da hukunci.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel