Kada ku dogara da gwamnati - Ministan Buhari ya yi kira ga matasa

Kada ku dogara da gwamnati - Ministan Buhari ya yi kira ga matasa

Ministan kwadago, Chris Ngige ya yi kira ga miliyoyin matasan Najeriya da basu da aikin yi da su kada su tsaya jiran gwamnati ta basu aiki domin kuwa bata da aikin da za ta iya basu, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito shi.

A maimakon jiran gwamnati, minista Ngige ya nemi matasa su kirkiri wasu sana’o’in da zasu yi domin fitar da kansu daga kangin rashin aiki, talauci da zaman banza, kamar yadda mai magana da yawunsa, Charles Akpan ya bayyana.

KU KARANTA: Gwamnan Borno ya yi ma Sojojin Najeriya kaca kaca bayan harin Boko haram a Auno

Minista Ngige ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a taron tattaunawa a garin Bini na jahar Edo inda aka tattauna a kan bambamci tsakanin manyan ayyukan gwamnati da kuma ayyukan zaman kai tsakanin daliban makarantun gaba da sakandari.

Ministan wanda ya samu wakilcin daraktan ayyuka na musamman a ma’aikatar kwadago, Martina Nwordu ya bayyana cewa dole ne matasa su kawar da kansu daga ayyukan gwamnati saboda masu kudin duniya a yau ba ma’aikatan gwamnati bane, mutane ne masu kirkire kirkire.

“Ministan ya yi kira ga matasa su yi amfani da basirar da Allah Ya yi musu wajen kirkiro abubuwa masu amfani da muhimmanci a fannoni daban daban domin taimakon al’umma. Ministan ya bayyana makasudin shirya taron a sassan Najeriya guda 4 shi ne don wayar da kawunan matasa game da muhimmancin sana’o’i da zaman kai.

“Don haka ya nemi dukkanin masu ruwa da tsaki su baiwa gwamnati hadin kai dangane da shirye shiryenta wanda take sa ran zasu fidda yan Najeriya miliyan 10 daga kangin talauci nan da shekaru 10 masu zuwa.” Inji shi.

A wani labarin kuma, rundunar Sojan kasa ta bayyana cewa ta ceto wasu dalibai guda uku daga hannun mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram bayan wata zazzafar gumurzu da musayar wuta da suka yi da juna a jahar Borno.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito babban kwamandan rundunar Soja dake yaki da yan ta’adda a yankin Arewa maso gabas, Manjo Janar Olusegun Adeniyi ne ya bayyana haka yayin da yake mika daliban uku ga iyayensu.

Adeniyi ya bayyana sunayen daliban kamar haka; Wommi Laja, Ammo Laja da kuma Kingi Laja, inda yace sun samu nasarar kubutar dasu ne bayan musayar wuta tsakanin yan ta’adda da wani hazikin Soja Laftanar Kanal Idris Yusuf, kwamandan Bataliyan Soja a Gubio.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel