Zainab Bulkachuwa ta kaddamar da sabon kotun daukaka kara a jahar Kano

Zainab Bulkachuwa ta kaddamar da sabon kotun daukaka kara a jahar Kano

Shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya, Mai Sharia Zainab Bulkachuwa ta kaddamar da wani katafaren sabon rassan kotun daukaka kara, wanda shi ne na rassa na 19 a Najeriya, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya.

Zainab ta bayyana cewa bude wannan rassa ya yi daidai da manufarta na ganin an warware shari’u cikin kankanin lokaci, tare da tabbatar da gaskiya da adalci a hukunce hukuncen da kotunan suke yankewa.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da fasinjoji 9 a kan hanyar Abuja

“Kotun daukaka kara na kokarin rage wahalhalun da ake fama dasu wajen yin doguwar tafiya da kashe makudan kudade wajen zirga zirga, kudin sharia da kuma daukan tsawon lokaci kafin a yanke hukunci, wannan ne yasa kungiyar lauyoyi reshen jahar Kano da gwamnatin jahar Kano suka yi korafi.

“Korafinsu kuwa shi ne yawancin shariun da ake yi a kotun daukaka kara na jahar Kaduna sun fito ne daga jahohin Kano da Jigawa, wannan ne yasa muka samar da sabon kotun daukaka kara.” Inji ta.

Zainab ta bayyana cewa a shekarar 1976 aka fara samar da kotun daukaka kara, rassanta na farko an samar da su ne a Legas, Enugu da Kaduna, zuwa 1977 aka kara guda biyu suka zama biyar, a Benin da Ibadan, amma a yanzu sun kai 18 bayan bude na Aba da Awka a yan kwanakin da suka shude.

“Rassa 8 sun fi sauran rassan cikowa, kuma daga cikinsu akwai kotun Kaduna, wanda yake wakiltar Kano, Jigawa da Katsina, amma muna fatan daga bude wannan kotun, zamu samu saukin gudanar da shariunmu cikin kwanciyar hankali.” Inji ta.

A nasa jawabin, gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa samar da kotun zai karfafa kasuwanci a jahar Kano, don haka gwamnati zata samu karin kudaden shiga, sa’annan yace samuwar kotun zai kusanta da adalci ga talaka, tare da karfafa zaman lafiya da lumana a jahar.

“Talaka bai cika daukaka kara ba komai yiwuwar samun adalci, bana jin dadin ganin ire iren mutanen suna shan wahala saboda rashin adalci. Babu shakka ina da tabbacin Mai Sharia Bulkachuwa ta yi aikinta yadda ya kamata a matsayinta na shugabar kotun daukaka kara.

“Abin alfahari ne yadda kika kammala zangon mulkinki ba tare da wata badakala ba, don haka muna taya ki fatan alheri a rayuwarki ta bayan barin aiki.” Inji shi.

Daga karshe Ganduje yace gwamnatin jahar Kano ta bayar da filayen da za’a gina rassan kotun na dindindin, filin na kallon sabon kotun, kuma yayi magana gwamnan jahar Jigawa sun amince zasu gina tare.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel